Wednesday, 7 November 2018
Tsare Ni Da Ake Yi Hauka Ne Da Rashin Hankali Da Cin Mutunci Da Kuma Cin Zarafi, Kamar Yadda Sheik Zakzaky Ya Bayyanawa Alkali Yau A Kotu

Home Tsare Ni Da Ake Yi Hauka Ne Da Rashin Hankali Da Cin Mutunci Da Kuma Cin Zarafi, Kamar Yadda Sheik Zakzaky Ya Bayyanawa Alkali Yau A Kotu
Ku Tura A Social Media

Daga Bilya Hamza Dass

A karo na biyu Shaik Zakzaky ya sake bayyana a gaban kotu domin cigaba da sauraron karar da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar dashi, bayan dage shari'ar da alkali yayi a wancan karon wanda jami'an tsaro suka bada uzurin matsalar karancin tsaro saboda zaman kotun yayi dede da ranar da Shugaba Buhari zai kawo wata ziyara garin na Kaduna, wanda yau kotun tasake zaman domin sauraron karar.

A wannan karon an kawo Zakzaky kotu bayan gabatarwa daga lauyoyi lauyan gwamnati ya karanto dalilin zaman daga bisani sai Alkali yafara karanto tuhume tuhume da akewa Shaik Zakzaky.

Sai dai a wannan karon yadda Shaik Zakzaky ke amsa tuhumar da ake masa ya nuna ya dau zafi sosai yana mai cewa “tuhumar da ake min haukane, rashin hankali ne kuma cin zarafi ne gareni”. Bayan alkali ya karanto tuhume ta biyu ya maimaita cewa wannan itace amsar shi. Daga karshe alkalin kotun yasake dage shari'ar zuwa 22/01/2019.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: