Wednesday, 14 November 2018
Sunayen Jaruman Kannywood Dake Goyon Bayan Atiku

Home Sunayen Jaruman Kannywood Dake Goyon Bayan Atiku
Ku Tura A Social Media
Sannu a hankali siyasa sai kara shiga duk sabgogi da kasuwancin jama’a ta ke yi. Irin wannan mamaya da siyasa ke yi ne ya saka jaridar Daily Trust yin wani sharhi a kan yadda goyon bayan Atiku da Buhari ya raba kan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.
A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, an samu rabuwar kai tsakanin jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood a kan goyon bayan manyan ‘yan takarar shugaban kasa; Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da shugaba Buhari na jam’iyyar APC.
Jaridar Daily Trust ta tattaro jerin jaruman Kannywood da tuni su ka fara yiwa Atiku kamfen. Ga jerin sunayen na su:

1. Sani Danja
2. Isa Feroz Khan
3. Bashir Nayaya
4. Maryam Booth
5. Fati Muhammad
6. Zaharaddeen Sani
7. Ummi Zee-Zee
8. Usman Mu’azu (Darekta)
9. Salisu Mu’azu (Darekta)
10. Hafizu Bello
11. Mustapha Nabruska
(ya dawo APC)
12. Abubakar Sani (Mawaki)
A bayan wallafa wannan jerin sunayen ne dai muka samu labarin Mustapha Nabruska ya Fice daga tafiyar Atiku Ya Dawo Tafiyar Buhari.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: