Monday, 26 November 2018
Sheikh Ahmad Gumi ya gargadi gwamnatin tarayya kan ci gaba da tsare El-Zakzaky

Home Sheikh Ahmad Gumi ya gargadi gwamnatin tarayya kan ci gaba da tsare El-Zakzaky
Ku Tura A Social Media
Shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya gargadi gwamnatin tarayya akan ci gaba da tsare shugaban kungiyar Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky inda ya bayyana hakan a matsayin babban barazana ga tsaron kasar.
Jaridar Thisday ta ruwaito cewa, a jiya Lahadi, 25 ga watan Nuwamba, Gum yayi kira ga gwamnatin tarayya kan ta saki shugaban kungiyar Shi’an don guje ma habbaka matsaloln tsaro da kasar ke fuskanta.

Ya ce ya zama dole gwamnati ta koyi wasu darusa daga yadda kungiyar yan ta’addan Boko Haram ya fara.


Zakzaky dai na tsare tun a watan Disamban 2015, tun bayan wani karo da mabinsa suka yi da rundunar sojin Najeriya a Zaria, jihar Kaduna. An yi zargin cewa sama da mambobin kungiyar 350 ne suka mutu a wannan karo.
An ci gaba da tsare Zakzaky duk da umurnin da kotu ta bayar na a sake shi wanda ya kai ga yawan zanga-zanga da karo tsakanin hukumomin tsaro da mabiyansa.
Gumi ya shawarci gwamnatin tarayya da ta sake shi domin guje ma billowar wata kungiya ta ta’addanci.
Da yake ci gaba da Magana, malamin na musulunci ya ce ya zama dole gwamnati ta mutunta umurnin kotu ta yi umurni ga sakin sa.
A cewarsa Zakzaky ya fara gane ikon gwamnati, da zaran ta sake shi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: