Tuesday, 6 November 2018
Ronaldo Ya Bayyana Dan Wasan Da Yake Son Sake Buga Wasa Da Shi

Home Ronaldo Ya Bayyana Dan Wasan Da Yake Son Sake Buga Wasa Da Shi
Ku Tura A Social Media
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Wayne Rooney, ya bayyana cewa har yanzu yana kewar buga wasa da Rooney kuma har yanzu shine dan wasan da yake son sake buga wasa dashi.
Ronaldo da Rooney dai sun buga wasa a tare a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United inda suka shafe shekara da shekaru suna buga wasanni kuma sun lashe kofuna da yawa a kungiyar.Sai dai Ronaldo wanda yabar Manchester United a shekara ta 2009 inda yakoma Real Madrid ya bayyana cewa Rooney dan wasa ne wanda yake taimakawa kowa da kowa a fili kuma baya gajiya idan yana buga wasa.
“Rooney babban dan wasa ne wanda kowa zaiso ace ya buga wasa dashi saboda yanada zuciya kuma ya kware wajen iya dukan kwallo sannan kuma idan yana fili zai dinga kara muku karfin gwuiwa” in ji Ronaldo
Ya ci gaba da cewa “Kasancewar Rooney a kungiya ba karamin abin alheri bane saboda yanada duk wani abu da ake bukata dan kwallo a yasamu kuma yanacin kwallaye na ban mamaki a kowanne lokaci"
A karshe Ronaldo ya bayyana cewa bai san abinda zai faru ba anan gaba amma watakila zasu iya sake haduwa anan gaba a wata kungiyar.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: