Wednesday, 14 November 2018
Maman 'Yan Nigeria Ki Gyara Kuskurenki Saboda Allah

Home Maman 'Yan Nigeria Ki Gyara Kuskurenki Saboda Allah
Ku Tura A Social Media


Maman 'yan Nigeria Hajiya Aisha Muhammad Buhari a jiya ta ziyarci kasar Qatar don gudanar da wani taro, amma sai dai a yadda ta bayyana babu ko gyale balle dogon hijabi gaskiya bamuji dadin hakan ba

Ya kamata da ace Mama Aisha tayi dubi da wannan mata balarabiya da suke tsaye tare don ta kara fahimtar ma'anar musulunci da sharadin da Allah Ya gindaya akan mata musulmi yadda zasu rufe surar jikinsu, Qatar kasar musulunci ne, inda ace Mama Aisha kasar kiristoci ko yahudawa taje zamu iya mata uzuri da tayi shigar bultu ne

Mama ta gyara wannan kuskuren, don wallahi dukkanmu zamu mutu kuma Allah Ubangijin musulunci da musulmai zai tayar damu don yin hisabi akan komai

Musulunci ya kasa iyaye mata kashi-kashi, mace tun daga haihuwarta har zuwa yarinta, balaga, shekarun girma da na tsufa, ana iya yiwa tsohuwar mace uzuri wanda abubuwan sha'awa na jikinta suka gushe, wato wanda zaisa idan na miji ya kalleta yaji sha'awarsa ta motsa, amma ya kasance ko da na miji ya kalleta sha'awarsa ba zata motsa ba saboda abubuwan sha'awa na jikinta sun gushe saboda tsufa, to irin wadannan mata tsofi ko da wani abu ya bayyana a jikinsu ba laifi bane, don haka su Mama a kiyaye umarnin Allah don Allah

Masu karin magana suna cewa gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba, so muke mu gudu tare mu tsira tare har a gaban Allah (SWT) gaba dayanmu

Allah Ka yafe mana Ka bamu ikon bin umarninKa Amin

Share this


Author: verified_user

0 Comments: