Monday, 26 November 2018
LABARI MAI DADI Sojojin Saman Nijeriya Sun Yi Wa Sansanin Boko Haram Ruwan Bama-bamai A Borno

Home LABARI MAI DADI Sojojin Saman Nijeriya Sun Yi Wa Sansanin Boko Haram Ruwan Bama-bamai A Borno
Ku Tura A Social MediaYau kwanaki hudu sojojin saman Nijeriya suke ruwan wuta a kan tawagar 'yan ta'addan da suka yi hari a sansanin sojoji dake kauyen Metele karamar hukumar Guzamala jihar Borno.

Jiragen yakin sojojin saman Nigeria kirar Mi-34M wani samfurin jirgin yaki ne wanda harsashin bindiga baya hudashi sunyi ruwan wuta daga sama da manyan bama-bamai masu linzami akan 'yan ta'addan, dukkan kayan yakin da suka dauka a sansanin sojoji dake Metele jiragen yakin sun lalata, kuma zuwa yanzu babu wanda ya tsira daga cikin 'yan ta'addan da sukayi harin.

Bayan 'yan ta'addan sun yi harin Metele suka kashe mana sojoji tare da kwashe kayan yakinsu, sai suka nufi kauyukan Tumbun-Rego da Kangarwa da Mainok a daidai lokacin da jiragen leken asiri ta sararin samaniya suka bi diddiginsu, kafin nan sai aka aiko da jiragen yaki dauke da bama-bamai da manyan bindigogi masu cin nisan dogon zango akayi kaca-kaca da tawagar 'yan ta'addan, wanda ya tabbata cewa babu wanda ya tsira daga cikinsu.

Hatta 'yan ta'addan da suka yi kokarin tsallaka bodar Nijeriya da makaman da suka samu a harin Metele jiragen yakin Nijeriya ya bi ta kansu an shefe su ba su samu hanyar tsira ba.

Bayanan sirri ya tabbatar da cewa kwamandojin 'yan ta'addan da sukayi hari a Metele ba 'yan Nigeria bane, akwai 'yan Algeria, Mali da Chadi, cibiyar ISWAP  wanda ISIS da kanta ta dauki nauyin harin.

Sojojin da suka tsira a harin Metele sunce sunji 'yan ta'addan suna magana da harcen Larabci da Faransanci, sun saka kayan sojoji irin wanda rundinar sojin hadin gwiwa na kasashe Multi National joint Task Force (MNJTF) tsakanin tsakanin Nigeria, Kamaru, Nijer da Chadi suke sakawa, da suka iso sansanin sojojin Metele su a tsammanin sojojin dake gurin sun dauka cewa 'yan uwansu sojoji ne suka kawo musu ziyara, kawai sai suka bude musu wuta.

Alhamdulillah su ma 'yan ta'addan basu tsira ba, Kuma yau kwana hudu kenan shugaba Buhari yana ta ganawa da manyan shugabannin tsaron Kasarmu Nigeria don ganin abinda ya faru a Metele bai sake faruwa ba.

Ina wadanda sukayi murna da abinda aka yiwa sojojinmu a Metele??? Insha Allahu murnanku za ta koma bakin ciki.

Allah Ka karawa sojojinmu taimako da nasara akan 'yan ta'adda manyansu da kananansu. Amin.

Daga Datti Assalafiy

Share this


Author: verified_user

0 Comments: