Sunday, 25 November 2018
KASHE-KASHE: Sheikh Bala Lau Ya Yi Kira Da A Tashi Tsaye Da Addu'o'i

Home KASHE-KASHE: Sheikh Bala Lau Ya Yi Kira Da A Tashi Tsaye Da Addu'o'i
Ku Tura A Social Media

Shugaban kungiyar IZALA, Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ya yi kira ga Limamai, Malamai, dalibai da ma dukkan musulmai da su tashi tsaye da addu'oi na neman Allah ya yaye mana fitintinun da suke addabar kasar Nijeriya na kashe kashen Rayukan Mutane.
Sheikh Bala Lau wanda ya bayyana haka a wani sako da ya fitar ta hannun mai magana da yawun sa, kuma shugaban kwamitin JIBWIS social media, Alhaji Ibrahim Baba Suleiman yace babu mafita da ya wuce addu'oi a halin yanzu.

"Muna kira da ayi addu'a a dukkan majalisun ilimi, da makarantun islamiyoyi na yara da mata da manya, ayi addu'o'i da alkunut a dukkan masallatai da khamsu-salawat
Sannan Limaman jumu'a suma su yi addu'oi a lokacin hudubar Juma'a" Inji Sheikh Bala Lau.
Shehin malamin ya kara da cewa lura da fitintinu da suka kunno kai a mafi yawan jihohin arewa kama daga Zamfara, Sokoto Kaduna Plateau, Adamawa, Taraba, Benue Yobe da kuma Borno, yace al'umma su koma ga Allah su nemi afuwa kuma su nemi Allah Ya yaye wannan bala'i.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: