Labarai

Karin Albashi: Gwamnoni sun ce A saurari Rage Yawan ma’aikata



Kungiyar gwamnonin Najeriya ta bayyana cewa idan dai har aka dage kan lallai-lallai sai sun biya karin mafi karancin albashi na Naira dubu 30, to fa gaskiya sai dai su rage yawan ma’aikatan su.

Shugaban gwamnonin na Najeriya Abdul Aziz Yari dake zaman gwamnan jihar Zamfara ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala wani zaman gaggawa da gwamnonin suka gudanar a jiya, garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.



Legit.ng Hausa ta samu cewa gwamnan ya kara da cewa Naira dubu 30 tayi masu yawa kuma ba su iya biyan ta domin a lissafin da suka yi ma, jihar Legas ce kadan zata iya biyan hakan ita ma don tana samun kudaden shiga da yawa ne ta hanyoyi daban.

Daga nan ne kuma ya ce tuni kungiyar sa ta nada wani kwamiti na musamman da zai gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a kan batun domin samun matsaya da kowa zai yi na’am da ita.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button