Monday, 12 November 2018
Kakanta Ba Ta Iya Sallah Saboda Rudewa Ko Za Ta Fadi Akanta? - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Home Kakanta Ba Ta Iya Sallah Saboda Rudewa Ko Za Ta Fadi Akanta? - Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Ku Tura A Social Media

Tambaya

Assalamu alaikum ina fatan Dr yana cikin koshin lafiya, Allah ya kara masa imani da fasaha Amin.Dr kakata ce tsufa ya kamata ga rashin lafiya, yaranta tara bata gane Ko daya daga cikin su gashi bata gane alwala balantana Sallah, Ko an mata alwala bazata gane Sallah ba, ga shi tana yini da pampas a jikinta ya zamuyi da sallanta???

Amsa

Wa alaikum assalam Ku yi iya ba-kin kokarinku wajan Ku ga ta kwatanta sallah, in bai yiwu ba ku kyale ta, saboda Allah ba ya dorawa rai abin da ba zai iya ba kamar yadda aya ta karshe a Suratul Bakara ta yi bayanin gamsashshe akan hakan.
A zahirin nassoshin sharia in har ba ta gane komai to za ta dau hukuncin Mahaukata ne, tun da ba ta cikin hayyacinta,
 mahaukaci  hadisi ya tabbatar da sarayuwar sallah daga kansa.

Sallah ba ta karbar wakilci, don haka ba Wanda zai rama mata a cikinku.

Allah ne mafi sani 

Amsawa✍🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

11/11/2018

®Darulfatawa.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: