Thursday, 15 November 2018
Ka Hukunta OSHIMOLE - DSS Ga Buhari

Home Ka Hukunta OSHIMOLE - DSS Ga Buhari
Ku Tura A Social Media


Hukumar tsaro ta jami'an farin kaya watau Department of State Services (DSS) ta shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya hukunta shugaban jam'iyyar sa ta All Progressives Congress (APC), Kwamared Adams Oshiomhole bisa karbar rashawa ta Dalar Amurka miliyan 55.

Shugaban jam'iyar APC, Adams Oshiomhole ya karbi cin hancin tsakanin dala miliyan 55 ko dala miliyan 80 daga hannun 'yan takara. An biya kudaden ta hanyar wakilai, ciki har da 'yar Oshiomholen.


Daga Yaseer Kallah

Share this


Author: verified_user

0 Comments: