Thursday, 29 November 2018
Ina Boko Haram Suka Samu Jiragen Yaki Masu Layar Zana?

Home Ina Boko Haram Suka Samu Jiragen Yaki Masu Layar Zana?
Ku Tura A Social Media


Rundunar sojojin Nijeriya ta bayyana cewa 'yan ta’addan Boko Haram sun fara amfani da jirage marasa matuka wajen kai farmaki a kan cibiyoyin tsaro na sojojin kasar.

Hukumar sojin ta ce ta kula cewa wasu mahara daga kasashen waje na shiga Nijeriya domin taimakawa kungiyar yan ta’addan a hare-hare da take kai wa jami’an tsaron kasar.

A cewar wata sanarwa daga hannun Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman, shugaban hafsan sojojin kasar, Laftanal Tukur Burutai ya ce yan ta'addan sun fara amfani da jiragen ne da kuma mayakan waje cikin watanni biyu zuwa uku da suka gabata.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: