Tuesday, 20 November 2018
Dalilai Takwas Da Suka Hana Yin Maulidi - Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano (Rahimahullah)

Home Dalilai Takwas Da Suka Hana Yin Maulidi - Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano (Rahimahullah)
Ku Tura A Social Media

1✏ Maulidi baya daga cikin Shariah, Yan Shi'a Fadimiyya ne suka kirkiro shi a Egypt.

2✏ Masana tarihi sun tafka sabani game da hakikanin rana da watan da aka haifi Annabi SAW. Wasu suka ce a Ramadan, wasu suka ce a Shabaan wasu kuma sukace a Rabi ul awwal.
3✏ Ta yaya zamuyi farin ciki da murna a ranar 12th Rabi al Awwal bayan a ranar ne Annabi S.A.W ya bar duniya? kuma babu sabani kowa ya yarda da hakan.

4✏ Bikin murnar zagayowar ranar haihuwa bashi da asali cikin Musulunci. Musulunci ya hana wannan.
5✏ Wannan biki baya daga Sunnah ko kuma Qur'an. Dukkan Ibadar da bata daga dayan biyun nan, to ba musulunci bane... Annabi SAW, "Na hore ku da kuyi riko da sunna ta da kuma sunnar khalifofina shiryayyu, ku guji fararrun al'amura, domin dukkan fararrun al'amura Bid'ah ne kuma dukkan Bid'ah bata ce. (Tirmizi 2676)"

6✏ Allah yana cewa a cikin [Surah al Maidah 3]. "A yau na kammala muku addininku." Tunda kuwa Musulunci ya cika ya kammala, waye kuma yake da wani da zai karo wani abu a cikinsa?

Kuma manzo s.a.w yace a hadisin Irbaady dan saariya.( kashedinku da fararrun al,amurra).

Kuma yace" wanda ya kirkiro wani abunda bayacikin al,amarin addinin mu an mayar masa."

7✏ Bikin maulidi koyi ne da Yahudawa da Nasara. Yahudawa na murnar haihuwar Uzair, Nasara suna murnar haihuwa Annabi Isa AS. Bayan kuma Annabi SAW yace, "Duk wanda yayi koyi da wata al'umma to yana cikinsu. (Abu Dawood)"8✏ Annabi SAW yace, " Ku bambamta ku sabawa mushirikai. (Sahih Muslim)".

Share this


Author: verified_user

0 Comments: