Sunday, 4 November 2018
Da Dumi-Duminsa: Hukumar Npower ta fara bankado tareda yin waje road da wasu wadanda suka shiga tsarin kuma Alhali Su Ma'aikata a Wurare Daban-Daban

Home Da Dumi-Duminsa: Hukumar Npower ta fara bankado tareda yin waje road da wasu wadanda suka shiga tsarin kuma Alhali Su Ma'aikata a Wurare Daban-Daban
Ku Tura A Social Media


Kamar yadda dai aka sani cewa aikin Npower aiki ne da gwaunatin tarayya ta samar domin tallafawa matasa da basuda aikinyi ne.

Haka kuma dokar data kafa hukumar ta haramtawa dukkanin wani wanda yake da ya shiga tsarin. Amma da yawan mutane sunki jin gargadin hukumar kuma suka cike fom din kuma har suna karbar kudaden Npower bayaga cewar suna aiki tareda karbar albashi a wasu ma'aikatun gwaunatin daban-daban.

To yanzu haka dai hukumar ta dukufa sosai wajen bankado irin wadannan mutanen tareda ciresu daga tsarin na Npower kuma hannutantasu ga hukumar yan sanda da dai sauran Jami'an tsaro.

Yanzu haka dai hukumar tayi nasarar bankado wasu daga jahohi daban-daban kamarsu jahar Kogi da Ebonyi.

Wadanda hukumar ta bankado yanzu haka daga jahar kogi sun hada da:

1. Alhassan Umoh Alhassan

2. Zubeiru Ali Bukari

3. Zakari Ali

Daga jahar Ebonyi Kuma akwai:

1. Itumo Sunday: Wanda Ma'aikaci ne a hukumar ADP ta jahar Ebonyi

2. Mbam Cletus Nwosike: Ma'aikaci a hukumar Shari'a ta jahar Ebonyi

3. Ogala Onyekachi: Ma'aikaciya a hukumar SEB CSC Ekwashi

4. Ogbaga Simon Nwalegu:   Ma'aikaci a hukumar samarda ruwan sha

Saboda haka hukumar tana kira ga duk wanda yasan shi Ma'aikaci ne a wani wurin kuma ya shiga tsarin da yayi gaggawar ficewa kafin hukumar ta kamashi kuma ta tamkashi ga hannun Jami'an tsaro tareda kuma wallafa sunansa duniya ta gani.

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: