Thursday, 8 November 2018
Da dumi-dumi: Atiku Ya karawa Dukkan Ma'aikatansa Albashi Mafi Karanci N33,000

Home Da dumi-dumi: Atiku Ya karawa Dukkan Ma'aikatansa Albashi Mafi Karanci N33,000
Ku Tura A Social Media


Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya yiwa dukkan ma'aikatan da ke karkashinsa karin albashi zuwa N33,000.

Mohammed El-Yakub, Direktan Gotel Communications, kamfanin sadarwa mallakar Atiku da ke Yola ya tabbatarwa Sahara Reporters a yau Alhamis inda ya ce, "za a fara biyan sabuwar albashin mafi karanci na N33,000 daga watan Nuwamban 2018. Kuma karin albashin ya shafi dukkan wadanda ke aiki karkashin Atiku har da masu hidima a gidajensa."

El-Yakub ya bayyana cewa a halin yanzu akwai kimanin mutane 100,000 da ke karbar albashi a kowanne wata a karkashin tsohon mataimakin shugaban kasar.

Atiku ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya amince da N30,000 a matsayin albashi mafi karanci kamar yadda kwamitin albashi da shugaban kasar ya kafa suka shawarci shi a cikin rahoton da suka gabatar masa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: