Monday, 19 November 2018
Cikin shekarun biyun farko, zan fitar da mutane miliyan 50 daga Talauci - Atiku Abubakar

Home Cikin shekarun biyun farko, zan fitar da mutane miliyan 50 daga Talauci - Atiku Abubakar
Ku Tura A Social Media

Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya kuma dan takarn kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Demcratic Party PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kaddama yakin neman zabensa na 2019 a yau Litinin, 19 ga watan Nuwamba, 2018.

Atiku Abubakar ya yi dogon jawabi ne ta shafi ra'ayi da sada zumuntarsa kan shirye-shiryen da zai aiwatar idan yan Najeriya suka zabeshi a 2019.Yace: "Shirye-shirye na zai samarwa ma'aikata albashi mai tsoka, Shirye-shirye na zai samarwa matasan Najeriya ilimi mai kyau, Shirye-shirye na zai karfafa mata, rage mutuwa ta hanyar haihuwa."

"Idan aka zabe ni shugaban kasa, zan zange dantse wajen jawo hannun jari da kuma taimakawa kananan masu kasuwanci miliyan 50 a fadin tarayya domin rubanya tattalin arzikinsu zuwa $900 Bilyan a 2025."

"Wadannan hannun jari zai samar da akalla ayyuka milyan 2.5 a kowani shekara, da kuma fitar da mutane milyan 50 daga cikin talauci cikin shekaru biyu."

"Na fara rayuwata maraya, mai sayar da itace a garin Jada dake Adamawa, amma Allah, yayinda amfani da Najeriya wajen zama abinda nake yau."

A bangare guda, shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da nasa yakin neman zaben 2019 a jiy Lahadi inda ya saki littafin shirye-shiryen nasa na abubuwan da yayi cikin shekaru ukun da ya shude.


Sources:legit.ng/hausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: