Tuesday, 13 November 2018
Badaƙalar Biyon Dala : Za Mu Hukunta Ganduje- Inji Buhari

Home Badaƙalar Biyon Dala : Za Mu Hukunta Ganduje- Inji Buhari
Ku Tura A Social Media


Ya Nunawa 'Yan  Najeriya Mazauna Faransa Yadda Ganduje Ya Rika Cusa Daloli A Babbar Riga.

Sha'aban Sharada Ya Nemi 'Yan Jaridu Su Binne Batun 

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya  gana da daliban Najeriya a Kasar Faransa. Wasu Dalibai daga jihar Kano sun yabawa Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje dangane da kokarinsa a harkar tallafawa Daliban Kasashen Ketare. 

Caraf, sai Buhari ya dakatar da su da cewa, "Shin ba ku ga bidiyon yadda Ganduje ya ke karbar cin hanci ba ne ya na cusawa a babbar riga?" Buhari ya kwatanta yadda Ganduje ya rika cusa Dala a babbar riga kamar yadda aka nuna a bidiyon. 

Shugaba Muhammadu Buhari ya ci gaba da cewa, "Mun ba Wa Jami'an tsaro bidiyon suna nazari matukar muka kama shi da laifi za mu dauki mataki".

Jaridar ta kara da cewa, Hadimin Shugaban Kasa akan harkokin Talabijin da Rediyo Sha'aban Sharada ya nemi 'yan jaridu su cire wannan magana da Buhari yayi kada duniya ta sani. 

Sha'aban Sharada dai a yanzu shine dan takarar Majalisar Wakilai a Jam'iyyar APC daga karamar Hukumar Birni.

Madogara:- Maje El-Hajeej Hotoro

Share this


Author: verified_user

0 Comments: