Friday, 16 November 2018
AREWA GIDAN SHASHANCI... Karanta wannan Abun Takaici

Home AREWA GIDAN SHASHANCI... Karanta wannan Abun Takaici
Ku Tura A Social Media

Yanzu da ace 'ya'yan Gwamna Yari aka dauke tuni sun dawo gida. Me ya sa? Saboda a matsayinsa na wanda yayi  shekara 8 yana kwasar dukiyar Zamfara. Ya halatta ya kwashi dukiyar jihar ya karbo su. 

Da 'ya'yan Shugaban Kasa aka sace da tuni sun dawo saboda me? Saboda ya halatta a kundin mulkin kasa a kwashi ko nawa ne a fito da su. 

Da har rige-rige Gwamnoni, Sanatoci da 'Yan Majalisar Wakilai za su rika yi wajen biyan Kudaden saboda a ce su masoyan Buhari ne. 

Da sayen fom din takara ne da ko Miliyan 1000 ne za su samu. 

Da bikin 'yar Gwamna za a yi sai ya gaji da karbar gudunmawar miliyoyin kudade. 

Da Sayawa Shugaban Kasa ko Gwamna tikitin takara ne da ka ji Kungiyoyi masu zaman kansu na fito da kudade. 

Da so suke su koma kujerunsu da ka ga ana yi wa Shugaban jam'iyyu ruwan kudade. 

Da bikin 'yar attajiri ake yi da ka ga ruwan masu kudi har da wanda ya fi kowa kudi a Afirka. 

Da ace a Kudancin Najeriya ne da tuni jaridu sun nemi kamawa da wuta ba tsaro har sai gwamnati ta biya sannan a kyale ta ta huta. 

Da ace a jihar da ake tsoron rasa kuri'a ne da wani zancen ake yi ba wannan ba. 

Da ace ba Musulmi ba ne da tuni suna dakunan iyayen su. 

Da ace wani Shugaba ne wannan masifar ta shafa da ka ga ruwan Malamai masu addu"o'i tare da kira da a yi Addu'a. 

Da ace wani abu ne ya taso zai raba wanda muke so da kujerar mulkinsa da tuni mun kunna wutar zage-zage da cin mutuncin juna a facebook. 

Amma da ya ke 'ya'yan Talakawa ne kuma KURI'UN su ba su da muhimmanci shiru kake ji. 

Allah Ya Zama Gatan Mu.


Madogara: Maje el-hajeej hotoro

Share this


Author: verified_user

0 Comments: