Wednesday, 21 November 2018
Allah Yayiwa Wani Fitaccen Daraktan Kannywood Rasuwa

Home Allah Yayiwa Wani Fitaccen Daraktan Kannywood Rasuwa
Ku Tura A Social Media
ALLAH ya yiwa fitaccen Mai bada UAMARNI a kannywood kuma mamallakin kamfanin SARAUNIYA FILM PRODUCTION DARAKTA AMINU MUHAMMED SABO rasuwa a ranat talata da dare Bayan doguwar jinya da yayi.

Aminu Muh’d Sabo

Za’ayi JANA’IZAR SA a gidan sa dake nan GWAMMAJA A ranar Laraba idan Allah ya kaimu da safe.
Marigayi Aminu Muhammed sabo, ya baiwa masana’antar Film gudummawa da dama A lokacin sa, Yayi kokarin baiwa JARUMAI Maza da Mata gudummawa a career su ta hanyoyi daban daban
Kadan daga chikin Fina finan da Marigayi Wanda ya bada UMARNI.
GAGARE, TANTIRI, NAGARI, ALLURA DA ZARE, DISKINDIRIDI, ZARGE, SANGAYA, GARWASHI.
ALLAH yaji kansa da rahama, Allah yasa bakin wahalar sa kenan ,Allah ka yafe masa kura kuran sa, kasa mutuwa ta zamo hutu a gare shi, tare da dukkan wanda yake ambaton LAH ILA HA ILLALLAHU MUHAMMADUR RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.

©filmhausa.com.ng

Share this


Author: verified_user

0 Comments: