Sunday, 18 November 2018
Abin Alfaharin Kannywood: Fim Din ‘Juyin Sarauta’ Ya Fafata Da Finafinai 1980 A Kasar Kenya

Home Abin Alfaharin Kannywood: Fim Din ‘Juyin Sarauta’ Ya Fafata Da Finafinai 1980 A Kasar Kenya
Ku Tura A Social Media

Daga dukkan alamu masana’antar shirin finafinai Hausa ta Kannywood ta fara nuna irin zakakurancin da ta ke da shi ba a cikin gida Najeriy ba, a’a, hatta a sauran kasashen Afrika. Wannan ya biyo bayan yadda fim Juyin Sarauta da a ka shirya a Kannywood ya fafata a bikin bajekolin da a ka gudanar kwannan nan a kasar Kenya mai suna Lake international PanAfrican Film Festibal. Wasu daga cikin finafinan Hausa su na gwada fasahar kirkirar labari da kwarewar iya direwar labarin da kuma daukar shirin, wato production, da iya salo da sarrafa hoto da zayyanar shirin, wato production design.

 Haka kuma a fili ta ke cewa, samar da labarai da su ka shafi al’adun kasar Hausa su na da tagomashi a wasu sasssa na Afrika da kuma duniya bakidaya. Lake international PanAfrican Film Festibal taro ne da a ke shiryawa duk shekara a kasar Kenya da ke gabashin Afrika. Wannan shi ne karo na uku da a ka gudanar da shi. Taron na bana an kai shi garin Nakuru, wanda shi ne birni na hudu wajen girma a kasar ta Kenya, nisansa daga birnin Nairobi ya kai kilomita 159. A bana finafinai 1980 a ka shiga wannan gasa da su daga kasashe 12 har da kasar Amurka. Kasashen da su ka shiga gasar kuwa su ne kamar haka: 

1.         Burkina Faso

 2.         Ethiopia 

3.     Ghana

4.  Kenya

 5.   Madagascar
 6.         Malawi 

7.         Najeriya

 8.         Senegal

 9.      Afrika ta Kudu 

10.   Amurka

 11.    Yuganda

 12.    Zambiya Fim din Juyin

 Sarauta ya na daya daga cikin finafinan da su ka samu zuwa matakin tantancewa na karshe, wato ‘nomination’ a matsayin Best Production Design, wanda wannan ba karamin abin alfahari ba ne ga masana’antar shirin fim da Hausa, idan a ka la’akari da cewa, hatta daga Amurka an samu finafinan da a ka shiga da su gasar, musamman idan a ka duba cewa, masana’antar shirin fim ta Amurka, wato Hollywood, ba ta da tsara a duniya. Taron dai an yi shi ne ranar 7 zuwa 10 ga watan Nuwamba, 2018.

 A lokacin wannan biki an gudanar da taron karawa juna sani da ajin koyarwa ga masu ba da umarni, wato ‘Master Class’ da taron tattaunawa a kan matsalolin da su ka addabi masu shirya finafinai ta fannin tallata hajarsu, da kuma batun yin hadin gwiwa tsakanin masu shirya finafinai na wadannan kasashe 12, da bajekolin fasaha da yawon bude ido a wuraren tarihi, kamar su Hyrad Hill da Lake Nakuru, don ganin namun daji da kuma tafkunan ruwa da hawa tsaunuka. A wajen taron an nuna finafinai (har da na yara) sama da 100 ciki har da Juyin Sarauta na Hausa, kuma shi ne fim (feature) daya tak daga masana’antar Kannywood da ya sami shiga wannan gasa. Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, daya daga cikin masu shiryawa kuma jarumin jarumai karo biyu a wannan shekara ta 2018 a cikin fim din Juyin Sarauta, shi ne ya sami halartar wannan wajen taro na kwana biyar a kasar ta Kenya, inda ya wakilci masu wannan shiri na Juyin Sarauta. 

Balaraba Ramat Yakub ce ta shirya fim din Juyin Sarauta, yayin da Falalu Dorayi ya bayar da umarnin shirin fim din na Juyin Sarauta. Bugu da kari kuma an samu wani shirin fim din zane na Hausa, wato cartoon, na Gizo da Koki, wanda wani matashi daga jihar Kano, Sulaiman Surajo, ya shirya shi ma daga masana’antar ta Kannywood.   

Share this


Author: verified_user

0 Comments: