Tuesday, 23 October 2018
Yan Fim Din Hausa Sun Fi Yan Jaridun Hausa Daraja A Mulkin Buhari

Home Yan Fim Din Hausa Sun Fi Yan Jaridun Hausa Daraja A Mulkin Buhari
Ku Tura A Social Media

Daga Fulani Shuaibu

JARIDAR DIMOKURADIYYA: Yadda Yan fil din Hausa Kannywood suka fi Yan Jaridun Hausa daraja a sabuwar Gwamnatin APC a karkashin jagoranci shugaban kasa Muhammad Buhari.

Babu wata ranar duniya da Jaridun Hausa baza su wallafa labaran yabo ga Shugaban kasa Muhammad Buhari ba, kuma duk lokacin da wani abu game da Gwamnatin Shugaba Buhari ya shigewa Al'umma duhu, jaridun Hausa sun dunga kokarin ganin sun samar da sahihan labarai har sai Al'ummar kasa sun fahimta.

Abun mamaki har yau babu wata lambar yabo ko kuma jinjinawa da Gwamnatin ke yima Yan Jaridun na Hausa bare ma har ayi batun gayyatar Yan Jaridun zuwa fadar Shugaban, abun mamaki wani lokacin Idan wani abu ya faru har fada ake yima Yan jaridun Hausa idan basu fito sun wanke Shugaba Buhari ba.

Hasalima Yan Fim din Hausa sun fi Yan Jaridun na Hausa daraja a Idon Gwamnatin da kuma sauran mukarraban Gwamnati tunda gashi an gayyace su tare da yi musu alkawura saboda muhimmancin su, cewa aka yi ai suna yima Buhari waka.

To Jaridun Hausa kamar su Hausa Times da Zuma Times da Mikiya da Jaridar Dimokuradiyya da Rariya da Madubi da Sarauniya da Arewa Daily Post da Zinariya da Arewar mu A Yau da sauran kafafen yada labaru su har yanzu basu taba baiwa Gwamnatin Buhari gudunmawa ba kenan?

Rahotanni sun bayyana yadda mukarraban Gwamnatin APC suka yima mawakan Hausa ruwan Dalar Amurka, wai saboda irin wakokin da suka dunga yima Gwamnatin APC wakoki a lokacin yakin neman zabe.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: