Thursday, 25 October 2018
Ta Faru Ta Kare : karanta Yadda Zaman Majalisar kano Tayi Da Jaafar Jaafar A Yau

Home Ta Faru Ta Kare : karanta Yadda Zaman Majalisar kano Tayi Da Jaafar Jaafar A Yau
Ku Tura A Social Media
#GANDUJEGATE

"Sunana Jaafar Jaafar nine Mawallafin Jaridar Daily Nigerian wacce ta wallafa bidiyon da aka nuna Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yana karbar na goro. 

Alkur'ani ne mai girma a tare da ni zan iya rantsewa da cewa wannan bidiyo gaskiya ne. Na ba wa kwararru sun tabbatar da sahihancin su. 

Akwai babban attajiri da ya kira ni ya kalli wannan bidiyon ya tabbatar min zai kai ni kasar waje ni da iyalaina. 

Shin zaka iya fada mana wannan Attajiri? 

A'a. 

Shin zaka iya fada mana sunan wanda ya ba ka bidiyon? 

Dokar aikin jarida ta hana fadi wanda ya kawo maka labari, sai dai idan a sirri za a zauna da shi ba a bainar jama'a ba. Sai mu duba doron doka mu ga Yadda za a yi. 

Shin zaka iya ba mu kwafin wadannan bidiyon? 

Eh zan iya ba ku. 

Ka Samu tsaro? 

Gaskiya na samu tsaro. 

Za mu zauna da kwararru su kalli wadannan bidiyo su fada mana sahihancin su.


Daga : Maje El-Hajeej Hotoro

Share this


Author: verified_user

0 Comments: