Wednesday, 3 October 2018
Surukin Shugaba Buhari, Muhd Indimi Ya Kori 'Yarsa Ameena Daga Kamfanin OER

Home Surukin Shugaba Buhari, Muhd Indimi Ya Kori 'Yarsa Ameena Daga Kamfanin OER
Ku Tura A Social Media

Makusantan Ameena Indimi za su misalta ta da mace mai saurin fushi da zafin rai. Idan baku manta ba, Ameena, wacce ake kira Yataka, ta tayar da hayaniya a lokacin da ake baikon yayan ta Ahmad da 'yar shugaban kasa Zahra, inda ita Yataka ta nace sai ta shiga da wayar salular ta fadan shugaban kasa, Aso Rock duk da cewa jami'an tsaro sun hana yin hakan.

Yataka a yayin sa'insa da jami'an tsaron ta nuna cewa tana so ta dauki bidiyon dukkan abunda zai gudana na baikon da kuma kayan tambaya da aka kawo da wayar ta. Duk da cewar hakan ya saba wa dokar fadar shugaban kasan. Duk da cewa wasu sun sanya baki yayin hayaniyar, Yataka ta ki sauraran jami'an tsaron.

A kwanan nan ne aka tsige Ameena daga mukamin ta na mataimakiyar shugaban kamfanin Oriental Energy Resources (OER). Baban ta, shahararren dan kasuwan nan Muhammad Indimi shine ya dauki matakin bayan Ameena ta kori manyan ma'aikata ba tare da sanin sa ba.  Ameena ta kori daraktan kamfanin da wasu masu taimakawa mashawartan mahaifin ta a fannin tattalin arziki.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: