Labarai

Hirar Waya Tsakanin ‘Yan Uwan ‘Yan Biyu Mata (TWINS) Da Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara

DAGA: Abdurrahman Abubakar Sada.

GA YADDA HIRAR TA KASANCE A TSAKANINSU:

Bayan ‘Dan Uwan Ya Gaisa Da ‘Daya Daga CiKin ‘Yan Biyun (Twins).

Kidnapper: Hello.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Mai gida ya gajiya.

Kidnapper: Lafiya lau.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Yaya gida ya aiki.

Kidnapper: An gode Allah.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: To barka dai Mai gida.

Kidnapper: Kai ne Mai gida ai.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Na’am.

Kidnapper: Kai ne Mai gida ai.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: A’a ka kai ne Mai gida ai Modibbo.

Kidnapper: Wane.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Ai yanzu kana gaba na sai yanda kayi da ni.

Kidnapper: A’a ina wane ni.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: A’a ai kai ne Mai gida ai, to yanzu Mai gida yaya kake son ayi, yanzu dai Mai gida kaga yaran nan Mai gida marayun Allah ne, ba uwa ba uwa, marayun Allah ne wallahi, ziyara suka zo garin.

Kidnapper: Nima nan da nika magana da kai maraya ne.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Wayyo Allah, toh, to duk Allah ya ji kan magabata.

Kidnapper: To Ameen.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Yauwa to ya za’a yi Mai gida.

Kidnapper: In kana son abunka, tun dazu na gaya maka Miliyan Dari Da Hamsin (150Million) zaku badawa.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: La IIaha Illallah Mai gida, Mai gida miliyan dari da hamsin (150M), mu duk danginmu, duk danginmu, ko mai miliyan guda babu, balle maganan miliyan dari dari da wani abu.

Kidnapper: To ku bar mana su kunjiya, diya mata masu kyau haka zaku tsaya kuna cewa wai minane minane.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Ai ba maganar haka bane ba Mai gida, diya mata mun sani ai ba haka bane, ba haka bane ba amma, amma ai kasan ana neman alfarma, ko ba haka ba? Tunda kai ai Oga ne, sai yanda kayi da mu yanzu.

Kidnapper: Tof yanzu ya kaka son ayi kai, miliyan dari kana ji ko? Yadda za’a yi ni da kai, ka bani miliyan dari gare su, me kar rage?.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: To Mai gida ni yanzu ina nigga wadannan kudin da kake kira, duk danginmu ba mai wannan kudin.

Kidnapper: To don Allah ni da kai kowa ya hankura da kiran wani kaji.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: A’a ba haka za’a yi ba, kaji ko? Ba za’a yi haka ba.

Kidnapper: To in ba haka ba ya kaka son ayi.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: To Mai gida ai yanzu komai yana hannunka, amman Mai gida mu duk danginmu ba mai wadannan kudin da kake kira, gabadaya danginmu ba mai wadannan kudin, kayi hakuri Mai gida, yaran nan marayun Allah ne, ka dai fadi yanda dai za’a iya.

Kidnapper: To ai nima dake maganar ai maraya ne.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Kai ma kanka maraya ne ko?.

Kidnapper: Kana ji ko? Kana ji ko?.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Ina jinka. Hello.

Kidnapper: Ka tsaya kayi magana mai kyau.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Eh! To naji Mai gida, amma ai sai ka fadi yanda zai yiyu ko? Ka dai san wadannan kudin da ka kira Mai gida bamu da da su kuma bamu da hanyarsu.

Kidnapper: TO don Allah kar ka sake kiran wannan lambar.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Yi hakuri Mai gida ai ba zancen haka bane ba, ai yanzu kai komai yana gare ka ne.

Kidnapper: Kai kana ji sai anjima tunda baka tashi ba.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: A’a na tashi mana, ba yanzu magana muke yi da kai ba.

Kidnapper: To magana ta banza banji wada abunda kace zaka ban ba, muna maganar banza, shine zaka ceman minane minane.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Ba maganar banza bace, ni yanzu ni na isa, Oga na kai ni inyi maganar banza da kai, ai ban isa ba, kai Mai gida na ne, kai yanzu Oga ne a waje na ai.

Kidnapper: Tunda kana Gusau ma ai kana iya kaman maganar banza.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: A’a ni a suwa, hah, ai ban isa ba, to duk inda nike Oga in kayi niyyar gani na ai dole inzo ka ganni, tunda kai yanzu Oga ne, ko ba haka ba?.

Kidnapper: Kai kana ji.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: Eh ina jinka.

Kidnapper: Yanzu ya za’a yi, ya kaka son ayi da kai?.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: To ai shine nike ce maka, Mai gida kudin da ka kira mu duk danginmu ba mai hanyar wadannan kudin.

Kidnapper: TO SAI ANJIMA.

Dan Uwan ‘Yan Biyu: YI HAKURI KA BARI MUYI MAGANA.

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN!

Mai bukatar hirar sai ya tuntube ni ta Inbox a WhatsApp, domin mallakar sautin ta.
WhatsApp Number:
07052904485

Allah ya sawake.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?