Saturday, 27 October 2018
Ganduje Ya Yi Sammacin Limaman Kano Sheikh Aminu Daurawa Sakamakon Huduba A Kan Bidiyon Karbar Cin Hanci

Home Ganduje Ya Yi Sammacin Limaman Kano Sheikh Aminu Daurawa Sakamakon Huduba A Kan Bidiyon Karbar Cin Hanci
Ku Tura A Social Media


Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

Jaridar NEWS DIGEST ta kawo rahoton cewa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya kirawo manyan limaman masallatan Juma'a na jihar Kano zuwa gidansa na kan titin Mayangu Road a daren Juma'a.

Jaridar ta yi rahoton cewa gwamnan ya zauna da limaman sakamakon wata huduba mai zafi da limamin masallacin Ansarul Sunna da ke Fagge Plaza, Malam Aminu Daurawa, ya gabatar inda yayi kira kan a gabatar da bincike a kan bidiyon da ya nuna "gwamanan na amsar cin hanci".

A sa'ilin da yake gabatar da hudubar, Malam Daurawa ya ce a yanzu bidiyo sheda ce da za a iya dogoro da ita yayin gabatar da bincike, inda ya yi misali da rikicin dan jaridar kasar Makka, Jamal Khashoggi.

Malamin ya ce: "Da shaidar bidiyo aka yi amfani gurin tabbatar da shigar Jamal Khashoggi cikin ofishin jakadancin Saudiyya na kasar Turkiyya.

“Ya kamata majalisar dokokin jihar Kana ta yi amfani da bidiyon gurin warware zargin cin hancin da ake yi wa gwamnan.

“Shekarau ya kasance gwamna na tsawon shekaru takwas. Ya kuma kasance minista. An bincike shi sannan an gurfanar da shi a gaban kotu. Saboda haka babu wani laifi don an binciki bidiyon."

Jaridar ta yi rahoton cewa, bacin ran da gwamnan ya samu sakamakon zazzafar hudubar ne ya sanya ya kirawo limaman domin ya gargade su a kan tsoma kansu cikin sha'anin siyasa.

“Ganduje bai ji dadin hudubar Daurawa ba. Saboda haka, domin ya dakatar da sauran limamai daga bin layin hakan, gwamnan ya kira su domin ya gargade su daga shiga sha'anin siyasa," inji wata majiya da ke da kusanci da sha'anin wadda ta zabi kar a bayyana sunanta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: