Monday, 1 October 2018
Duniya Ta Yi Rashin Babban Malamin Musulunci

Home Duniya Ta Yi Rashin Babban Malamin Musulunci
Ku Tura A Social Media

Daga Dr. Mansur Sokoto

Allahu Akbar!

Girma da daukaka sun tabbata ga wanda ba ya gushewa.

A yau duniyar Musulmi ta yi rashin wannan babban Malami, masani kuma fitaccen marubuci dan kasar Saudia, Sheikh Sa'd bn Wahf Al-Qahtani wanda ya wallafa littafai da yawa, amma karamin littafinsa 'Hisnul Muslim' na addu'oi ya game duniya da yaruka daban daban. 

Ya rasu da sanyin safiyar yau Litinin 21 ga Muharram 1440H (01/10/2018) a babban birnin Riyadh, kuma za ayi jana'izarsa da la'asar a babban Masallacin Rajhi a kai shi makabartar An-Nasim.

Allah ya jikan sa da rahama, ya sa aljanna ce mahadarmu da shi.

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: