Sunday, 7 October 2018
Atiku Abubakar Ya Lashe Zaben Fidda Gwani A Jam'iyar PDP Na Shugaban Kasa

Home Atiku Abubakar Ya Lashe Zaben Fidda Gwani A Jam'iyar PDP Na Shugaban Kasa
Ku Tura A Social Media
Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ne ya lashe zaben fidda na gwani na jam’iyyar PDP.
Atiku ya fafata da ‘yan takara 11 na jam’iyyar, PDP, ‘yan takarar sune tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan Kaduna Ahmad Makarfi, gwamnan jihar Gwambe Ibrahim Dankwambo, Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, David Mark tsohon shugaban majalisar Dattijai, Bukola Saraki shugaban majalisar dattijai, Alhaji Tanimu Turaki, Alhaji Datti Baba Ahmad, David Jang, tsohon gwamnan jihar Filato.

Atiku Abubakar din ne ya lashe kuri’u  1,532 mafiya rinjaye, a yayin da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yake biye da shi da 693.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: