Saturday, 20 October 2018
Ali Nuhu Ya Nada Nafisa Abdullahi A Matsayin Uwargidan Kamfinsa

Home Ali Nuhu Ya Nada Nafisa Abdullahi A Matsayin Uwargidan Kamfinsa
Ku Tura A Social Media
Shahararren Jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sarki Ali Nuhu, ya nada fitacciyar jaruma, Nafisa Abdullahi, a matsayin uwargidan kamfaninsa na shirin fim. A wani sako da ya saki a shafinsa na dandalin sada zumunta (Instagram), Ali Nuhu, ya bayyana cewar ya nada jarumar a mukamin ne saboda kwarewar ta a cikin shirin fim. 

"Ma'anar uwargida shine wata mace da ta zama daban. Ta fara shirin fim tun daga kasa har ta samu daukaka zuwa fitacciyar jaruma da ta lashe kyauta masana'antar Kannywood. 

Ta zama jaruma saboda gogewar da take da ita a harkar fim. Ina mai gabatar ma ku da Nafisa Abdullahi a matsayin uwargidan kamfanin shirya fina-finai na FKD," kamar yadda Ali Nuhu ya rubuta. Kamfanin shirya fina-finai na FKD ya dade yana fitar da fina-finai da da su ka yi fice masana'antar Kannywood. 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: