Tuesday, 23 October 2018
Abubuwan Da Suka Haɗani Da Obasanjo - Inji Buhari

Home Abubuwan Da Suka Haɗani Da Obasanjo - Inji Buhari
Ku Tura A Social Media

1. Ya turo min da sunayen mutane domin a naɗa su ministoci har sau biyu, amma ban aminceba.

2. Ya turo min sunan wanda zai maye gurbin shugaban hukumar NIA amma ban gamsu ba.

3. Hakanan ya turo min da kamfanin da za'a bawa aikin wuta na Mambila wanda zai ci kuɗi kimanin $5.8 billions, shima dai ban yarda ba.

4. Tun bayan dana ɗare karagar mulki na fahimci gwamnati ce ke biyan albashin ma'aikatan gidan gonar sa na Ota, nan ma dai na dakatar da shi.

5. Hakanan na gano cewa yana amfani da ababan hawa na gwamnati a makarantun Bell da Jami'a tun lokacin da yake mulki domin cin ma muradun sa, shima na dakatar da wannan.

Laifukan Obasanjo ba za su lissafu ba kuma laifukan sa yake tsoro domin ya kiyaye mutuncin sa a gaba.

Wadannan dalilan suka sa Obasanjo ke kalubalantar salon mulkina a koda yaushe kamar inda jaridar Faces International Magazine ta rawaito.

Inji Buhari

Share this


Author: verified_user

0 Comments: