Friday, 5 October 2018
Abubuwa 4 na sanyawa Mace Tabo Mara gogewa a zuciyarta idan namiji ya aikata mata su.

Home Abubuwa 4 na sanyawa Mace Tabo Mara gogewa a zuciyarta idan namiji ya aikata mata su.
Ku Tura A Social Media

(Matsalolin gidan Aure).

(1)Nuna halin ko in kula yayin data Ke cikin tsananin jinyi ko wani rashin lafiya,bayan ta warke ka dawo ka nuna kana yi da ita.

(2)Nuna halin ko in kula lokacin da take cikin laulayin ciki ko Naquda .

(3) Goranta mata idan kayi mata wani abu na kyautatawa  ko bajinta yayin da wani abu na sa6ani ya hada Ku.

(4)zagin iyayenta ko aibanta su,ko wulaqanta 'yan uwanta.

Wadannan abubuwa 4 da wuya mace ta yafewa namiji su a cikin zuciyarta, koda ta yafe a zahiri saboda darajan Aure ko 'ya'ya,kuma suna haddasa kiyayya me daci da zafi a zuciyar 'ya mace ,koda bata furta ba toh abin yana nan yana damunta aranta.Allah yasa maza masu wannan dabi ar suyi haquri su gyara,Ameen.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: