Wednesday, 5 September 2018
Ya Zama Wajibi Shugaba Muhammadu Buhari Ya Wadata 'Yan Nijeriya Da Abinci, Domin Ba A Hakurin Zama Da Yunwa" - Inji Dr Ahmad Ibrahim Buk

Home Ya Zama Wajibi Shugaba Muhammadu Buhari Ya Wadata 'Yan Nijeriya Da Abinci, Domin Ba A Hakurin Zama Da Yunwa" - Inji Dr Ahmad Ibrahim Buk
Ku Tura A Social Media

Daga Abdurrahman Abubakar Sada

Wannan kira ya fito ne daga bakin Babban Malamin Addinin Musulunci, Sheikh  Dr. Ahmad B.U.K Kano

Shehin Malamin ya ci gaba da cewa: "Lallai a samarwa al'umma abinci, kar a bar ta cikin yunwa, matukar aka bar al'umma cikin yunwa, kafin lokacin da za a zo a samu dama a gyara idan an samu damar, wadansu sun tagayyara, wadansu sun tozarta, wadansu rayuwa ta halaka su, kuma duk sai Allah ya tambayi mutum, sai Allah ya tambaye ka wadannan mutane duk da ke karkashin ka, kasancewar ka kana siyasa, ko kasancewar ka kana mulki, ba abinda aka dauke ma cikin hakkoki na shari'ar Musulunci. Shi ya sa halin da al'umma suka kai yanzu na yunwa, ya kai na mutane fa suna tagayyara, wadansu dukiyar su sun karye".
.
"Wadanda ake maganar cewa sune suka kawo tabarbarewar tattalin arziki, wadansu da suke wahala yanzu suke halaka ba su da hannu a cikin wannan, to mene ne laifin su. Mutane sun kai yanzu, duk sa'adda aka yi barazana aka kori yara Makaranta, lokacin Jarabawa, sai kaga duk inda za a nemo kudi a biya su za a nemo a biya su, yanzu haka, jarabawar da ta wuce, yara in an kore su, da yaro ya je gida sai uban shi ya ce zauna yanzu ta ciki ake ba ta Makaranta ba, ba ta Kudin Makaranta ba, wani daga nan karatun ya tafi kenan ba shi ba daman Karatu".
.
"Shi ya sa abin da ake nema wajen masu mulki, wajen Shugaban Kasa Mai cikakken iko, nan zuwa sati (mako guda) duk inda Allah ya ba ka Mulki ka wadata su da abinci, duk karkashin mulkin ka inda Allah ya dora ka a kansu a ga ka wadata su da abinci, abinci ba ya daukan jinkiri a jira zuwa Lokaci kaza.
Shi ya sa Allah (Madaukakin Sarki) ya ce: "Allazi Ad'amahum Min Ju'in Wa Amana Hum Min Khauf", kashin bayan rayuwa abubuwa guda biyu ne; Aminci da Abin ci, Abin ci da Aminci, da'iman abubuwa guda biyu su ke tafiya".
.
"Shi ya sa mu na kyautata zato, muna fata kan nan zuwa sati insha Allahu, duk Nijeriya za ta cika da abinci, Shinkafa ta kara kudi, Masara ta kai inda ba ta kaiwa ba sai wannan Lokaci, kuma wadannan duk matsaloli ne Allah ya na kallon bayin sa".

"Zantuttukan da ke hana ruwa gudu su ne maganganun 'yan Siyasa, magana ce gaskiya, maimakon a fada wa Shugaba ya maida hankali ya yi, sai a maida shi Siyasa, ana suka ana zagi, wannan ba shi zai fishshe mu ba, wannan sai ya hana ma su son su fadi gaskiya ma ba za su iya fada ba, idan sun fada sai wadancan su ja zare, wannan ya fadi kaza wannan ya fadi kaza, shi kuma wanda ake son ya yi gyara din, ya san wadancan maganar banza ce su ke",
Sako Za Ta Isa Insha Allahu - Inji Dr. B.U.K.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: