Thursday, 27 September 2018
Siyasa A Musulunci Da Kuma Siyasa A Kasata Nigeria - Faisal Nasir Muhammad

Home Siyasa A Musulunci Da Kuma Siyasa A Kasata Nigeria - Faisal Nasir Muhammad
Ku Tura A Social Media
Fitowa Ta Daya (01)
📌Siyasa dai kalmace ta larafci, kuma abinda take nufi shine gudanar da al'amuran mutane da jagorancinsu a bisa wani tsari da zai kaisu ga cimma Wata manufa. 

Shiyasa wani mai hikima yake cewa :

فبينا نسوس الناس والأمر أمرنا ... إذا نحن فيهم سوقة نتنصف.

Yake cewa " A yayinda da Mune muke jagorantar mutane se gashi a yau mu ake jagoranta". 

Wanda kuma dama Wannan itace Siyasa watarana kana shugaba wata Rana ana shugabantarka.

Sannan babu Inda kalmar Siyasa tazo a cikin Quran Amma tazo a cikin hadisin Annabi saw Inda yake cewa a hadisin da Abu Huraira ya rawaito" كَانَت بَنُو إسرَائِيلَ تَسُوسُهُمُ الأَنْبياءُ، كُلَّما هَلَكَ نَبِيٌّ خَلَفَهُ نَبيٌّ، وَإنَّهُ لا نَبِيَّ بَعدي، وسَيَكُونُ بَعدي خُلَفَاءُ فَيَكثُرُونَ"

Wato Banu Isra'il sun kasance Annabawa sune suke musu jagorancinsu a cikin al'amuransu a bangaren addini da kuma Rayuwa....."

📌 Zamu fahimci haka a rayuwar Annabi Musa Wanda yazo a matsayin annabi kuma Mai fafutukar Siyasa, ta yadda fir'aun yake jagoranci a Kasar Misrah, Saboda ganin yakai wani mataki yasa yake ganin zai kalubalanci Allah, hakan tasa Allah ya umarci annabi Musa daya kalubalanci fir'un ta Fuskar addini da kuma Rayuwa. 

📌 Annabi saw yayi jagoranci a Makka Shekara 13 Sannan yayi hijira zuwa madina Inda ya zama shugaba na addini da kuma Siyasa a Tsawan Shekaru 10, Wanda shine yake jagora ta kowane bangare na addini da kuma fanin rayuwa, ya zama kuma shine mai sanya doka tare da hukunta wanda doka tahau kansa a madadin Allah swa. 

Annabi saw a jagorancinsa da yayi akan siyasa ta muslunci ta yadda yake cewa a sabawa Yahudawa da Nasara, Wanda dama siyasar muslunci ta maida hankali kan bangaren Ruhi Wanda siyasar da bata muslunci ba ta maida hankali akan gan-gar jiki, Wanda dama anfi bukatar a gina Ruhi Sannan a gina jiki daga baya, kamar yadda annabi saw a makka ya fara gina Ruhin mutane Inda a makka kuma ya maida hankali akan gan-gar jiki, Akwai markel heards dan America yayi rubutu akan mutane 100 da sukafi kowa mahimmanci a rayuwar dan Adam tare da chanza musa rayuwa  seya fara kawo Sunan annabi Muhammad saw, da aka tambayesa Saboda me yayi Haka se yace ba ina magana akan addini bane da addini nake magana sena saka annabi Isa amma ina magana ne akan wadanda sukayi fice a duniya Shiyasa nasa Annabi Muhammad saw Wanda kuma shine Wanda ya kafa abinda har yau babu Wanda zai iya rushe Shi Shiyasa nasa annabi Muhammad saw, kuma annabi isa Shima yayi Siyasa ta Hanyar shugabantar mutanan sa Amma a yau Kiristoci basa amfani da irin nasa, Amma irin jagorancin da musulmai suke kai shine irin Wanda annabi saw yayi, Shiyasa har yau musulmai suke amfani da Salan siyasarsa wajan zabar shuwagabanni musamman a kungiyoyin musulmai. 

Misali a muslunci ana zabar shugabane ta Hanyoyi guda uku [3] 
_______________
1: Ayyanawa ta Hanyar wadanda sukafi kowa hankali da fada aji daga cikin mutane, a irin Wannan tsarin ne Sayyadina Abubakar ya zama Khalifa dama sayyadina Usman da Sayyadina Aliyu.

2: Idan shugaba zai mutu Ya Nada shugaba Wanda zai kasance bayansa, a irin Wannan tsarin sayyadina umar ya zama Khalifa Lokacin rasuwar Sayyadina Abubakar.

3: Yin amfani da karfi wajan Nada wani shugaba, ta Hanyar Adalchi ko kishiyarsa kamar yadda hakan ya faru duk a Tarihin muslunci, ta yadda wani mai adalchi zai hambarar da Azzalumi seya hau mulki, ko kuma wani Azzalumi ya hambarar da wani mai adalchi seya hau Mulki.

Yanzu duk a cikin Wannan tsarin guda 3 da ake zabar shuwagabanni a muslunci bashi bane tsarin Democracy, domin ba kowane yake zabe ba, kuma babu Zangon Mulki, kamar yadda ba,a sauke shugaba a muslunci seda wasu dalilai kamar yin ridda, fasikanci da kuma Rashin lafiya wadda take kaiwa ga gushewar hankali da makamantan su. 

📌 Wannan shine tsarin siyasar muslunci kuma Manzon Allah saw shine ya fara assasa siyasar muslunci misali.
_________________
1: Annabi saw Bayan ya zama shugaba na addini da kuma rayuwa a Madina, seya dinga Sawa Sahabbansa tsoran Allah musamman idan ya basu wani shugabanci domin kuwa sunsan hukuncin cin kayan daba nakaba, Amma idan a democracy ne to dama babu wannann tsarin Sedai abinda kundin tsarin mulki ya shirya, ta hanyar sabatta juyatta da duniyar wadanda ake shugabanta. 

📌 Anan zamu fahimci cewa Manzon Allah saw ya gina Siyasarsa da addini sabanin Democracy Wanda suke ganin Siyasa daban Addini daban, kamar 👉 Ansawr Assadat: shugaban masar  mai taken: babu addini a Siyasa kuma babu siyasa a addini. 

2: Maida hankali akan zaman lafiya shine Inda annabi saw yafi maida hankali bayan Tauhidi, domin idan kanada aqida kanada zaman lafiya ka gama samun nutsuwa.

3: hukunta Mai laifi dukmin girmansa da mukaminsa da matsayinsa, Shiyasa sanda wata mata tayi sata yace Koda Fadima yarsa ce tayi to seya yanke mata hannunu. 

4: Sanin mutanan sa Kake jagoranci, kamar yadda annabi saw yasa aka taba yimasa kidayar mutanan sa yake mulka a madina.

5: Karfafa tinanin mutane ta wajan yin karatu da rubutu domin Larabawa basa karatu basa Rubutu kafin zuwan Muslunci, har sayyadina umar yace Akwai makocinsa Bayahude daya iya rubutu kuma yanada amana, amma haka akwai shugabanci babu magatakarda a lokacin  har seda akai Badar aka Kama mayaka, Sayyadina Abubakar ya bada shawara da su koyar da musulmai karatu da rubutu domin su fanshi kansu.

📌 Anan zamu fahimci cewa zaka iya rike wani matsayi a karkashinka yayinda Kake shugaba har zuwa Sanda zaka samu Wanda Kake ganin ya can-canta Koda kuwa za'ace maka baba Go Slow, sannan kuma yana nuna tsadar Ilimi Yafi komai tinda gashi koyar dashi zaisa firsina ya yanta kansa.

5: Habbaka Tattatalin Arziki, ta yadda ya fara da Kudin ganima a irin haka har arzikinsu ya yalwata, tare da mai karfi yasha taimakawa mara karfi, tare da hana Roko da zaman banza, hakan yasa suka tashi suka naimi na kansu. 

📌 A irin Wannan salon siyasar ne Kalifofin da suka biyo bayan Annabi saw sukai Shugabancinsu har addinin yakai Inda yakai harya cika duniya har a zamanin khalifancin Umar bin Abdul'azeez za'a tara Abinci a rasa mabukata Saboda tsabar wadata kowa yanadashi baya bukatar karba. 

Wannan shine kashi na farko insha Allah Anan gaba zamu dora da Siyasa a Kasata Abar Alfaharina Nigeria. Allah muke roko daya bamu shugabanni na gari a ko wane mataki. 

✍️            Faisal Nasir Muhammad

17/01/1440__27/09/2018

Share this


Author: verified_user

0 Comments: