Friday, 21 September 2018
Muhimman Abubuwa Biyar (5) Da Yakamata Ka Sani Game Da Ado Gwanja

Home Muhimman Abubuwa Biyar (5) Da Yakamata Ka Sani Game Da Ado Gwanja
Ku Tura A Social Media
Ado Isa Gwanja wanda aka fi sani da Ado gwanja, jarumin barkwanci ne a dandalin masana'antar Kannywood kuma hazikin mawaki ne.
Jarumin wanda tauraron sa na cigaba da haskawa a fagen nishadantarwa ya samu karbuwa a zukatan masoya masu bibiyan fina-finan hausa.
Hakazalika yana da farin jini a fagen waka musamman daga mata duba da irin wakokin biki da yake rairawa. Bisa ga wannan dalilin aka yi masa lakabi da 'limamin Mata'.
Advertisement
Mawakin yana daya daga cikin fitattun yayyan kamfanin White house Family wanda Adam A.Zango ke jagoranta.
Sanin kowa ne cewa Zango maigidan sa ne hakazalika shima mawakin baya boye ma jama'a dangatakar dake tsakanin su.
Mun kawo maku wasu abubuwa biyar da muke son ku gane dangane da jarumin kamar haka;

1. Shi ruwa biyu ne

Duk da cewa shi dan asalin jihar Kano ne, Mahaifin sa dan garin Warawa ne dake Kano kuma mahaifiyar sa yar kabilar shuwa Arab ce daga jihar Borno.

2. Karatun sa

Ado Gwanja yayi karatun firamaren sa a makarantar Babbangij i dake Karkasara . Sannan yayi karatun sakandare a Sakandiren kofar Nasarawa .
Bai samu ya cigaba da karatun sa bayan bayan Sakandare. Bayan rasuwar mahaifin sa jarumin ya shiga buga-bugar rayuwa har Allah Ya kawo shi zuwa ga matsayin da yake yanzu.

3. Harkar waka ya fara.

Yawanci ana ganin cewa jarumin ya fara da harkar sai dai a yanda ya bayyana, ya fara aiki a masana'antar nishadi ta fagen waka. Yace sama da shekaru 12 yake waka sai dai kuma a wancan lokacin ba'asan shi kana bai samu kudin shiga situduyo ba don buga waka.

4. Wanene gwanin sa

Hakika dangantakar shi da sauran mawaka mai kyau ce kuma akwai girmamawa tsakanin, mawakin yace babban gwanin sa a wannan harkar shine mawaki Aminu Maidawayya.

5. Dalilin da yasa ya fiye yin wakar mata

Sanin kowa ne cewa hazikin mawakin ya fiye yin wakokin biki wanda ana iya cewa wakokin mata ne sai dai mafi yawanci ba'a san dalilin da yasa ya shahara a wannan fagen ba wanda yasa ma har ake kiran sa da 'limamin mata'.
A cewar shi dalilin da yasa yake yin wakokin mata shine domin mata sune iyayen biki kuma masu iya magana sukan ce inda baki ya karkata ta nan yawu kan zuba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: