Friday, 21 September 2018
Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Bayyana Dalilin Da Yasa Anka Daina Ganinta A Fim Yanzu

Home Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Bayyana Dalilin Da Yasa Anka Daina Ganinta A Fim Yanzu
Ku Tura A Social Media
Ta bayyana hakan ne yayin da take bada amsar tambayar da wani masoyin ta yayi a shafin ta na Instagram.

Fitacciyar jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi ta bayyana dalilin da yasa ba'a cika ganin ta a cikin fina-finai a kwana-kwanan nan.

Jarumar bayyana hakan ne a yayin da take baiwa wani masoyinta amsar tambayar da yayi mata na cewa, mai yasa bata cika fitowa a fim kwana-kwanan nan?.
Masoyin jarumar ya yayi tambayar bayan ya sanar mata cewa ita ce jarumar wanda fim dinta yafi birge shi kuma yana kewar rashin ganin ta a sabbin fina-finai dake fitowa daga masana'antar kannywood.


Nafisa ta mayar masa da martani inda take cewa ta gode da soyayyar da yake mata kana ya shaida masa cewa tana da wasu ayyuka da take yi bayan fim kuma harkar tana da matukar wahala idan ta hada da fim domin shirya fim tana daukar lokaci kuma tana da wahalar hadawa. Tace idan ta samu labari mai kyau zata iya tsaida matsaya game da batun fitowa a shirin.

Daga karshe jarumar ta wasa masa ruwan sanyi a zuciya inda tace yayi hakuri zuwa cikin watan Disamba zai ganta a cikin shirin fim.

Sources:pulsehausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: