Wednesday, 26 September 2018
Farawa da iyawa Ahmed Musa Ya Samu kyautar Gwarzon watan Agusta a Saudi Arabia

Home Farawa da iyawa Ahmed Musa Ya Samu kyautar Gwarzon watan Agusta a Saudi Arabia
Ku Tura A Social Media
Gabanin wasan firemiya na kasar wanda kungiyar sa ta buga da tawagar Al-Taawoun ranar Litinin 24 ga wata aka mika masa kyautar.

shiga kasar Saudiya da kafar dama, ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na watan farko na gasar firemiya na kasar.

Gabanin wasan firemiya na kasar wanda kungiyar sa ta buga da tawagar Al-Taawoun ranar Litinin 24 ga wata aka mika masa kyautar.

Tauraron dan wasan tawagar Super Eagles na cigaba da haskawa bayan komawar sa kungiyar Al-nassr daga Leicester na Ingila.

Wasan sa na farko a kungiyar, Ahmed Musa ya zura kwallo a raga a wasan su da Al-jazira wanda aka tashi 2-1, Al-nassr ta samu galaba.
Kungiyar sa ta samu nasara a wasan inda ta doke abokin adawar da kwallo daya babu ko daya.

Dan wasan yana daya daga cikin fitattun yan wasa dake taka leda a kasar kana ya samu kyakkyawar tarba daga masoya a kasar.
Ahmed Musa ya samu wannan kyautar mako daya bayan da ya taimaki kungiyar sa da kwallo uku a ragar abokan adawar su.

©pulse.ng

Share this


Author: verified_user

0 Comments: