Tuesday, 25 September 2018
Dole Sai Muna Kai Hare-Hare A Wasanninmu Na Gida -Pogba

Home Dole Sai Muna Kai Hare-Hare A Wasanninmu Na Gida -Pogba
Ku Tura A Social Media
Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Pogba, ya bayyana cewa dole sai kungiyar ta dage tana yawan kai hari musamman idan tana buga wasa a gida idan har suna son sukai ga gaci.

Pogba ya bayyana hakane bayan kungiyar ta tashi daga wasa 1-1 da kungiyar kwallon kafa ta Wolverhampton a wasan sati na biyar na gasar firimiya da a yanzu ake bugawa.

Manchester United dai tasamu maki daya ne kacal cikin wasanni biyu data buga a filin wasanta sai dai kuma ta samu nasarar wasanni uku data buga a waje akan kungiyoyin Burnley da Watford da kuma kungiyar Young Boys a gasar zakarun turai

Idan muna buga wasa kawai babu abinda za mu dinga tunani sai dai kai hare-hare saboda bamu da inda yafi gidanmu kuma munfi samun dama a gida kamar kowacce kungiya saboda haka akwai bukatar sake lissafi” in ji Pogba
Ya ci gaba da cewa  “kungiyoyi suna jin tsoronsu idan suna buga wasa a gida saboda haka dole sai suna yawan gudu a fili suna kai hari ba sassautawa kamar yadda mukayiwa Liverpool da Chelsea da Tottenham a shekarar data gabata”

A yau ne dai kuma Manchester United za ta buga wasanta na gaba da kungiyar kwallon kafa ta Derby County, wadda tsohon dan wasan Chelsea da Ingila, Frank Lampard yake koyarwa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: