Saturday, 8 September 2018
Dama Dabi'ar Mawakan 'Yan Siyasa Ne Cin Zarafi 'Yan Jam'iyyar Adawa Ya kamata su Rarara su yi koyi da Aminu Ala

Home Dama Dabi'ar Mawakan 'Yan Siyasa Ne Cin Zarafi 'Yan Jam'iyyar Adawa Ya kamata su Rarara su yi koyi da Aminu Ala
Ku Tura A Social Media


Daga Datti Assalafiy

Wasu jama'a suna ta tambaya ta har a comment wai ya batun wakar da Rarara yayi mai taken "Malam ya ci kudin Makamai" tunda gashi yau Asabar Malam Ibrahim Shekarau zai koma jam'iyyar Baba Buhari Maigaskiya, to ya batun wakar Rarara?

Wato jama'a mu fahimta su mawakan 'yan siyasa hake suke, dabi'ar su ce su ci mutuncin babban 'dan siyasar da sun san ba zai ba su kudi ba ko an biya su su yi wakar cin mutunci, haka sana'ar tasu ta koya musu, ko wanda yake rike da madafun iko suna masa waka yana basu kudi idan ya sauka daga mukami wani abokin gabansa ya hau ta zasu sake wancan su dawo wajen wannan, kuma suyi waka su zagi wancan, haka dabi'arsu take

Nazifi Asnanic yayi waka wa Jonathan Mai taken "su Jonathan suke so" amma kunga da gwamnati ta kubucewa Jonathan ya dawo yayiwa shugaba Buhari waka, ni haka nake ban taba goyon bayan wani mawaki da yake cin mutuncin tsoffin masu gidansa ba, domin na tabbata watarana zai iya yin waka yaci mutuncin gwanina a siyasa

Kuma ina tabbatar muku a yau mulki ya kubucewa shugaba Buhari ba abin mamaki bane mawakansa su juya masa baya idan sabuwar gwamnati ta biyasu suyi waka suci mutuncin shugaba Buhari, wallahi ba abin kunya bane wannan a gurin mawakan 'yan siyasa, maroka ne kudi suke nema itace sana'ar tasu, baku da masaniyar cewa wasunsu har bin bokaye sunayi suna kuma yiwa junansu asiri?

Sannan wadanda suke kauce kauce don Allah ku dena, mu fito mu fadi gaskiya itace soyayya don Allah, Rarara da yace Malam yaci kudin Makamai ai da Malam Ibrahim Shekarau yake, kunga gashi yau zaiji kunya, kuna kusa dashi don Allah ku bashi shawara ya gyara, ina tare dashi a wasu wakokinsa amma bana tare dashi a wasu wakokinsa na cin mutunci, kunga dai babu irin alherin da Kwankwaso bai masa ba, amma sai da yayi waka yaci mutuncinsa daga baya, wannan kuskure ne a fada masa ya gyara, ita harkar siyasa ba kayan gado bane

Don ku kara fahimtar dabi'ar mawaka bari na baku misali; Jama'a ku tuna da jam'iyyar PDP tun farkon lokacin da aka kafata a wajajen karshen shekarar 1990s Haruna Aliyu (KK) Ningi shi yayi waka mai taken "PDP jam'iyyata" har wakan ta yadu a duniya akasan jam'iyyar ta PDP, amma don ku kara fahimtar hatsarin mawakan siyasa shi dai wannan Haruna Aliyu KK yazo daga baya yayi wata waka mai take "PDP Shegiyar Uwa Mai kashe 'Ya'Yanta", to wannan itace asalin dabi'ar mawaka, maroka ne ba sana'ace da suba sai wakar, kuma suna wakar ne ga inda zasu samu kudi

Zan so a ce su Rarara su yi koyi da dabi'ar mawaki Alhaji Aminu Alan Waka, bayan wakoki masu ma'ana da yake ba zaka tabaji yaci mutuncin wani ba saboda wani

Bana shakka wannan sakon zai isa inda ya dace, Muna fatan su Rarara zasu dauki darasi sannan su gyara kuskurensu.

Allah Ya taimakemu gaba daya Amin

Share this


Author: verified_user

0 Comments: