Wednesday, 5 September 2018
Dalilin Da Yasa Zan Taimakawa Zainab Indomie -Inji Adam A Zango

Home Dalilin Da Yasa Zan Taimakawa Zainab Indomie -Inji Adam A Zango
Ku Tura A Social Media
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adamu Abdullahi Zango ya bayyana cewa a yanzu ya kammala shirye-shirye don taimaka wa jaruma Zainab Abdullahi wadda aka fi sani da Zainab Indomie don ceto ta daga mawuyacin halin da ta shiga bayan ’yan fim sun yi watsi da ita.
Zango ya bayyana haka ne a lokacin da ya sanya hoton jarumar a shafinsa na Instagram, sannan ya sha alwashin yin duk abin da zai yi don martabar jarumar ta dawo a masana’antar fina-finan Hausa.
Zango wanda ake kira da Fresh Prince ya ce ’yan fim da dama sun jefar da jarumar bayan sun ci moriyarta, sun jefar da ita irin yadda ake yasar da kwaure a lokacin da aka ci moriyar ganga.
Ya ce, jarumar ta shiga cikin mawuyacin hali, inda ’yan fim suka yi watsi da ita a lokacin da take bukatar taimakonsu.
“A yanzu na shirya yin komai don in dawo da martabarta, zan yi haka ne a lokacin da mutanen da suka ci moriyarta suka yi watsi da ita,’ inji shi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: