Friday, 21 September 2018
Classiq Arewa Mafiya Ya Raya Ranar Haihuwarsa Da Sabon Album "The New North"

Home Classiq Arewa Mafiya Ya Raya Ranar Haihuwarsa Da Sabon Album "The New North"
Ku Tura A Social Media
Hazikin mawakin hausa hip-hop Barnabas Buba Luka wanda aka fi sani da Classiq ko Captain sama yana murnar zagayowar ranar haihuwar sa yau 21 ga watan Satumba.
Domin raya wannan rana mai muhimmi a rayuwar shi, mawakin zai fitar da faifan sabbin wakokin shi domin nishadin masoyan sa da masu bibiyan wakokin sa.

Kamar yadda ya sanar a shafin sa na Instagram mawakin wanda aka yi ma lakabi da 'Arewa mafia' zai kaddamar da wakokin ne a wajen taron biki da aka shirya masa musamman domin murnar ranar haihuwa.

Sabon faifan wakokin shine "The New North" kuma wakoki Takwas ne a cikin ta.
Wasu daga cikin mawaka da ya saka a cikin ta sun hada da Ice Prince Zamani, Ckay da Yung L.

Kasancewa yau take ranar haihuwar shi ne ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da shi ;

1. Dan jihar bauchi
Wannan mawakin da aka haifa ranar 21 ga watan Satumba na 1991 haifaffen dan jihar Bauchi ne kuma shine da na karshi cikin yara 3 da iyayen sa suka haifa.

2. Baban shi malami ne
Kwarrai ko kana iya kiran shi da “dan mallam” domin shima na alfahari da haka kasancewa babban shi malami ne a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake nan jihar Bauchi. Baban shi likita ne na boko a fannin ilimin “geography” ita kuma uwar sa malama ce a asibiti.

3. Yayi karatun sa a Arewa
Shidai wannan jarumin waka ya fara karatun sa na firimari garin Bauchi kuma ya kammala karatun digiri dinsa a jami’ar Ado Bayero dake
Kano inda yaa karanta ilimin kwamfuta.

4. Ya yayi wasa a garuruwa da dama kuma jakadan arewa ne
Classiq ko kuma “arewa Mafia” kamar yadda yake ma kansa lakabi yayi wasa a wurare da dama kuma ya yi waka tare shahararrun mawakan Nijeriya .

5. Duk wakar shi akwai dangantaka da Arewa
Ko cikin baitutukar shi ko sunnan wakar ko kuma yanayin shigar shi a bidiyo zai ka ji ko ka gan abun da ya ganganci arewa. Duk da cewa wannan mawakin yana iya basaja ya koma wakokin turanci amma ya amince da ya dabbaka yaren ga idon duniya.
yayi wakoki irin su Zauna, Sama, hoto, barka da sallah, Ana haka da dai sauransu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: