Saturday, 4 August 2018
Wasu kurakurai a fim din Mu Zuba Mu Gani

Home Wasu kurakurai a fim din Mu Zuba Mu Gani
Ku Tura A Social Media
Suna: Mu Zuba Mu Gani
Tsara Labari: Ibrahim Birniwa
Kamfani: Mia Enterprises
Shiryawa: Muhammad Mia da Abubakar Bashir Mai Shadda
Bada Umarni: Kamal S. Alkali
Jarumai: Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Jamila Nagudu, Fati Washa, Hauwa Waraka, Teema Yola, Asma’u Nas da sauransu.
Sharhi: Hamza Gambo Umar
Ginshiki
A farkon fim din an nuna Maimuna (Hauwa Waraka) ta shiga gidan kawar ta Sakina (Jamila Nagudu) inda ta nuna wa Sakina rashin jin dadin ta a kan mijinta da zai kara aure ba tare da Sakina ta fada mu su ba. Nan fa Sakina ta nuna ba ta son maganar cewa mijin ta zai kara aure ba, kuma ta’ki yarda da hakan har sai da Maimuna ta nuna mata katin shaida sannan ta amince.
Sanin hakan ne ya sa Sakina ta tunzura ta soma mamakin cin amanar da mijinta zai ma ta domin ta dau kudi ta bashi don su yi kasuwanci amma ya dauka ya je ya ‘kara aure da kudin. Nan ta fita zuwa wajen mijin nata Ahmad (Ali Nuhu) wanda ta tarar ya gama shirin fita don zuwa shagalin biki, amma har a sannan bai nuna mata cewar aure zai yi ba, jin furucin bakin sa ne yasa ta ‘kara tabbatar da abinda take zargi, hakan yasa ta debo manja ta watsa masa a kan sabuwar shaddar dake jikin sa kuma ta nuna masa ta riga ta gama gane shirin sa, nan suka fara musayar yawu har suka nufi cikin daki inda Ahmad ya shiga wanka don sauya kayan jikin sa, hakan ne ya bawa Sakina damar kulle shi a cikin daki sannan ta dau wayar sa ta nufi wajen ‘kawar ta Maimuna wadda ta kawo mata labari suka fita daga gidan da nufin zuwa gidan mahaifiyar Ahmad su kai mata ‘karar sa......
Har zuwa karshen fim din.

Abubuwan birgewa:

1- Labarin ya nishadantar kuma ya rike me kallo ba tare da gajiyawa ba.
2- Jaruman sun yi ‘kokari matuka wajen isar da sakon labarin.
3- An yi ‘kokarin samar da wurare masu kyau wadanda suka dace da labarin.
4- Sauti ya fita radau, abin daukar hoto wato camera itama ba laifi.

Kurakurai:
1- Lokacin da Sakina ta watsawa mijin ta Ahmad manja a rigar sa har ta biyo shi cikin daki tana yi masa masifa, Me kallo yaji ta kira sa da suna Mahmud, shin Sakina ta mance sunan mijin ta Ahmad ne da har ta kira sa da Mahmud?

2- Shin Nabila bata da iyaye ko kuma dangi ne? Duk da irin matsalolin da suka faru musamman a lokacin auren ta amma ba’a nuna iyaye ko kuma wasu dangin ta ba.

3- Mai kallo yaga Nabila ta dawo gidan Sakina da zama a sanda take matsayin amarya, da nufin ba zata koma hannun Ahmad ba har sai ya biya Sakina kudin ta, ba’a nuna lokacin da Nabila ta kwaso kayan ta daga gidan da Ahmad ya kama mata haya ba, shin kayan Sakina take sakawa?

4- Har fim din ya ‘kare ba’a nuna wa mai kallo irin sana’ar da Ahmad yake ba, shin Ahmad ba shi da aikin yi ne? Kuma wacce irin kwangila ce Ahmad yayi wadda har ya samu miliyan arba’in? Tunda ba’a nuna Ahmad yana wata sana’a ba ya kamata ayi bayanin irin kwangilar da yayi ya samu kudi masu yawa haka, idan kuma shi ma’aikaci ne wanda aka kore sa daga wajen aiki, to ya dace a yiwa mai kallo bayani ko da baki ne.

5- Lokacin da Ahmad yaje wajen mahaifiyar sa da maganar cewa zai ‘kara aure saboda matan sa biyu sun hade masa kai, a matsayin mahaifiyar sa wadda aka nuna a uwa ta gari, bai kamata ta bashi shawarar cewa idan ya ‘kara aure ya saki matar sa Sakina ba. Domin duk da sakin aure ba haramci bane, to amma abu ne wanda ko ubangiji ba ya son shi.

6- Akwai wurare da yawa wadanda muryoyin jaruman basu hau da bakin su ba, kamar lokacin da a ‘karshen fim din su Sakina suka yi nadamar abinda suke yiwa mijin su, da kuma lokacin da mahaifiyar Ahmad taje gidan amaryar sa Jamila da safe a karo na biyu, duk muryoyin su basu hau da bakin su ba.
Karkarewa:
Fim din ya nishadantar, amma daga ‘karshe sabon zaren labarin da aka tufka yaso tsinkewa, saboda an kawo karshen fim din tun labarin bai gama direwa ba. Allahu A’alamu.!

Share this


Author: verified_user

0 Comments: