Wednesday, 29 August 2018
Tsokaci Kan Sabon Shirin Fim Din‘Ba Kama'

Home Tsokaci Kan Sabon Shirin Fim Din‘Ba Kama'
Ku Tura A Social MediaA jiya ne kamfanin shirya finafinai na Kwankwaso ya saki tallan sabon fim dinsa mai suna Ba Kama a kafafen sadawar zamani, domin dai a bi tsari da duniyar finafinai ke tafiya a kai. Fitar wannan tallan ya janyo hankalin dubunnan mutane ma su sha’awar kallon finafinan Hausa.
Tallan fim din ya kayatar da mutane matuka da gaske, musamman da yake an ga sabbin abubuwan da ba a saba gani a Kannywood ba.
Kwankwaso Movies, Kamfani ne da ya samu sahalewar hukumar ba da lasisin Kamfanoni ta ƙasa, kuma yana ɗaya daga cikin Kamfanonin da suke samar da ingantattun fina-finan Hausa don amfanin jama’a maza da mata.

Ga duk mai bibiyar harkokin masana’antar shirya fina-finan Hausa wato tsangayar Kannywood, ya kwana da sanin samun sabon canji da ake kokarin samarwa duba da yadda sauran masana’antun samar da fina-finai na duniya suke a kan tsari na ci gaba a ko da yaushe, don haka wasu daraktocin ke ganin bai dace muma a bar mu a baya ba.

Shi dai wannan fim mai suna Ba Kama, yana ɗauke da salon na musamman wanda zai ƙayatar da al’umma, kasancewar an yi amfani da ƙwaƙwalwa wajen tsara zubin labarin da kuma jaruman da za su fito a cikin fim ɗin.
Da yake zantawa da wakilinmu game da fim ɗin, Darakta Yaseen Auwal ya ce, haƙiƙa fim din an daɗe ba a ga irinsa ba, domin ya sha bamban da irin finafinan da suke fitowa kasuwa yanzu. A cewarsa, tsarin da aka bi na ɗaukar fim ɗin da kuma kasuwancinsa ba kamar yadda aka saba gani ba ne.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: