Wednesday, 1 August 2018
Tsige Bukola: Shugabancin APC da Sanatocin jam’iyyar sun gana da Buhari

Home Tsige Bukola: Shugabancin APC da Sanatocin jam’iyyar sun gana da Buhari
Ku Tura A Social Media


Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewar shugaba Buhari da ragowar shugabannin jam’iyyar sun amince cewar shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya kamata a ajiye mukaminsa, tun day a bar jam’iyyar.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowa daga wata ganawa da shugaba Buhari da kuma Sanatocin APC da aka yi da yammacin yau, Laraba.

Rahotanni sun bayyana cewar an yi ganawar ne tsakanin masu ruwa da tsakin na APC biyo bayan ficewar da ‘ya’yan jam’iyyar ke yi.

A cewar Oshiomhole, “tun da ya bar gidan sarauta, to idan ya san mutuncin kansa sai ya ajiye rawaninsa domin na gidan day a bari ne”.

Oshiomhole ya kara da cewa, “koma menene dalilin, zamu iya fita jam’iyya amma ba zamu iya fita daga Najeriya ba. Amma ga duk mutumin da ya san abinda ya kamata, to zai yi abinda ya dace koda ya canja shawara.”

A halin yanzu jam’iyyar APC ce keda mafi rinjayen mambobin majalisar dattijai da mutane 53, adadin day a zarce na jam’iyyar PDP da APGA.

Shugaban na APC ya ce tuni sun san cewar Saraki da wasu da suka dawo APC zasu fita daga jam’iyyar domin wasu daga cikinsu ma sun fito sun fadi cewar zasu fice duk da basu sanar da lokacin fita ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: