Wednesday, 29 August 2018




Karanta Amsar Da Nafisa Abdullahi Ta Baiwa Wasu Da suka Tambayeta Yadda Ta Mance Da Mutuwar Mahaifiyarta A KWANA 14

Home Karanta Amsar Da Nafisa Abdullahi Ta Baiwa Wasu Da suka Tambayeta Yadda Ta Mance Da Mutuwar Mahaifiyarta A KWANA 14
Ku Tura A Social Media

Kwana goma sha hudu kenan da rasuwar mahaifiyar tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi, muna fatan Allah ya kai Rahama kabarinta. Nafisar ta saka wadannan hotunan nata a dndalinta na sada zumunta saidai wasu na ganin cewa yayi wuri ace ta fara mantawa da rasuwar mahaifiyartata.

Tambaya :- Wani, ya tambayi Nafisa cewa, har kin gama jimamin(mahaifiyar taki) Ko? Allah ya kyauta.

Amsa :- Nafisa ta mayar mai da martanin cewa, na gama nuna muku.

Tambaya:- Haka watama ta tambayi Nafisar dan Allah ta taimaka mata ta gaya mata yanda ta yi saurin mancewa da rasuwar mahaifiyartata da wuri haka, domin tana bukatar kwarin gwiwa irin na Nafisar.

Amsa:- Nafisa ta amsa mata da cewa, babu wanda zai iya mantawa da mahaifanshi, har yanzu ina jin kamar zanga ta kirani a waya, nasan tana kallon komai, kuma ba zata so ta ganni a ko da yaushe cikin rashin kwarin gwiwa ba, shiyasa nake kokarin ganin na kasance yanda zata so ganin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: