Sunday, 19 August 2018
CANJA RANAR BABBAR SALLAH Musulman Nijeriya Za Su Rana Azumi Daya Idan..., Cewar Sheikh Dahiru Bauchi

Home CANJA RANAR BABBAR SALLAH Musulman Nijeriya Za Su Rana Azumi Daya Idan..., Cewar Sheikh Dahiru Bauchi
Ku Tura A Social Media

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce idan ya tabbata an ga watan Ramadan da ya wuce a yammacin Talata amma aka ki bayyana labarin ga Musulmin Nijeriya don a yi daidai da Saudiyya wajen daukar azumi to Musulmin Nijeriya za su biya azumi daya na ranar Laraba.

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana haka ne lokacin da majiyarmu ta Aminiya ta tuntubi Shehin Malamin game da takaddamar da ta taso kan jikirta ranar Babbar Sallar bana, inda watan Zul-kida yana da kwana 28 Kwamitin Ganin Wata ya bayyana washegari 1 ga Zul-Hajji, don komawa aiki da ganin watan Saudiyya.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, saboda wadanda alhakin sanar da ganin wata ke hannunsu a Najeriya ba addini suka karanta ba shi ya sa suke ganin saukin hadarin abin. “Da a ce sun karanta addini ne da sun san akwai Yaumi Shakki a lokacin da duniya ba ta hadu wajen kafofin watsa labarai ba. Na biyu da a ce an karanta addini da an san madala’in ganin watan ’yan Najeriya ba daya ne da na Saudiyya ba, saboda haka akan iya yin azumi daya zuwa biyu wani sa’in, kafin Saudiyya ta dauki azumi,” inji shi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, abin da ya kamata a gane filin samaniya na ko’ina daban ne, “Mukan dauki azumi a Najeriya in mun je Kaulaha sai mu cika azumi 30 su ba su ga wata ba, sai mu fada wa Shehu Ibrahim (Radiyallahu anhu) mu ce masa yaya za a yi mu mun cika azumi 30 kuma a nan kasar Senegal ba a ga wata ba? Sai Shehu ya ce mana, Shehu ya ce a Najeriya ku sai da kuka ga wata kuka dauka muka ce masa ce.

Sai ya ce to gobe ku kada ku yi azumi kuma kada ku sha ruwa, wato sai a ajiye niyyar azumin kuma ba za ku ci abinci ba. Wato ya zama kamar kamun baki, wato kamar a garinku kai ba ka ga wata ba gari ya waye aka tashi da azumi ka ga kai da ba ka ga wata ba, ba za ka sha ruwa ba don ana azumi kai kuma ba ka yi niyyar azumi ba, sai ka kama baki.

Haka in azuminka ya cika amma inda kake ba a ga wata ba sai ka kama baki ba azumi ba cin abinci. Allah ne Yake da kowane filin sama da ake ganin wata kuma kowane filin sama na kowace kasa da lokacin ganin watansa da Allah Ya sa.”

Shehin ya ce sai a ji wadansu suna cewa a dauki na Makka, alhali saman ganin watan Makka daban da na ganin watan Najeriya. “Idan lokacin ganin watanku ba daya ba ne dole ku saba da su a samu bambanci. Amma na Idin Layya nan ne ake bin kasar Makka don ba inda ake da Arfa sai Makka din don haka ba za mu yi Layya ba, ba za mu yi Idin Layya ba sai bayan sun yi Arfa,” inji shi.

Ya ce addini nassi ne a farko sannan imani ya biyo baya, sai hankali ya biyo bayan imani. “Amma a ilimin zamani hankali ne a gaba a cikin duk sha’anonin rayuwa. Idan aka dawo kan abin da ya shafi Najeriya da Saudiyya a kan watan Zul-Hajji a nan ana amfani da lissafin ganin watan Saudiyya ne don ita take da Arfa a duk duniya. Saboda haka kowa zai bar lissafinsa ya bi na Saudiyya saboda su suke da filin Arfa domin ranar 8 ga lissafinsu ake fita filin Muna don fara aikin Hajji.

Idan alhazai suka kwana ranar 9 su tafi filin Arfa idan sun dawo Muzdalifa suka kwana wayewar garin 10, sai duk duniya a tashi da Sallar Layya. Saboda haka lissafinsu ne ake amfani da shi a watan Zul-Hajji, saboda su suke da filin Arfa, sabanin watan Ramadan wanda ba sai an jira ganin Saudiyya kafin a dauka ba,” inji Shehin.

Sheikh dahiru Bauchi don haka idan aka yi Arfa ran 9 watan Zul-Hajji, ya zamo ke nan washegari dukan Musulmi su karrafa bakin Allah da suka yi Hajji suka hau Arfa, a yi yanka ranar goma ga watan Zul-Hajji, wannan yanka ana yin sa ne duk duniya don a karrama bakin Allah da suka yi Hajji sunan yankan Layya amma bakin Allah ake karramawa a yi Idi a gode wa Allah, ranar goma ga Zul-Hajji ranar Babbar Sallah.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: