Labarai

Yanzu An Gama Da Boko Baram, Saura Gyara Yankunan Da Suka Barnata, Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yanzu yankin arewa maso gabas yana matakin daidaita lamurra bayan rikicin Boko Haram.

Da ya ke jawabi ga sojojin Nijeriya a garin Munguno a ziyarar da ya kai jihar Borno a ranar Juma’ar da ta gabata, Buhari ya ce “ta tabbata cewa yanzu muna cikin mataki ne na kokarin daidaita lamurra bayan rikici Boko Haram, kuma hakan ya samu ne saboda kyakkyawan aikin sojojinmu”.

Shugaba Buhari ya kuma kara da cewa mayakan Boko Haram da kansu suke mika wuya, kamar yadda kamfanin dillacin labaran AFP ya ruwaito.

Bayanin shugaban a Munguno kamar yana nufin an kawo karshen tashin hankalin da jihohin arewa maso gabashin Nijeriya suka yi fama da shi a kusan shekara tara.

Rundunar sojin Nijeriya da gwamnatin Buhari sun dade suna ikirarin kawo karshen rikicin Boko Haram wanda ya yi sanadin salwantar dubban rayuka a arewacin Najeriya tare da raba miliyoyi da gidajensu.

Tun a yakin neman zabensa, Buhari ya alwashin zai kawo karshen rikicin Boko Haram da ya shafi kasashen da suka kewaye tafkin Chadi, Nijar da Kamaru da Chadi.

Sai dai kuma har yanzu Boko Haram na ci gaba da yin barazana a yankunan inda ko a watan da ya gabata an kashe mutane 43 a hare haren kunar bakin wake da aka kai a garin Damboa a jihar Borno.

Kashe-kashen da ake samu a rikicin makiyaya da manoma da kuma harin ‘yan fashi a wasu jihohin Nijeriya wani babban kalubale ne na tsaro ga Buhari wanda ya ayyana neman wa’adin shugabanci na biyu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button