Tuesday, 10 July 2018
Tsohuwar ministan Nijeriya Amina Muhammad ta samu sarautar "Sarauniya" a jamhoriyar Nijar

Home Tsohuwar ministan Nijeriya Amina Muhammad ta samu sarautar "Sarauniya" a jamhoriyar Nijar
Ku Tura A Social Media
Tsohuwar ministan muhalli karkashin shugabancin shugaba Buhari kuma mataimakin sakataren majalisar dinkin duniya, Amina Muhammed, ta samu sarautar "Sarauniya" a kasar jamhoriyar Nijar.

Jakadiyar Nijariya a majalisar dinkin duniya ta samu sarautar ne yayin da ta kai ziyarar aiki kasar kashen makon da ya shude.

Da wannan sabon nadin da ta samu, tsohuwar ministan zata shiga daga cikin masu bada umarni game da shugabanci a kasar tare da bada shawara ko gudunmawa.

Minsitan ta kai ziyara kasar ne domin gudanar da wasu ayyuka ta musamman domin taimakawa al'ummar kasar musamman mata da yara kanana.

Ta hadu da shugaban kasar Jamhoriyar Nijar,
Mahamadou Issoufou, da uwardakin sa tare da sauran ma'aikatan majlisar shugaban.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: