Tuesday, 31 July 2018
Tijjaniyya Ta Yi Hanun Riga Da ‘Yan Hakika, Inji Shaikh Dahiru Bauchi

Home Tijjaniyya Ta Yi Hanun Riga Da ‘Yan Hakika, Inji Shaikh Dahiru Bauchi
Ku Tura A Social Media
Shaikh Dahiru Usman Bauchi, Shararren Malamin addinin Islama ne a fadin Nijeriya dama Afrika baki daya, a gefe guda kuma shugaban darikar Tijjaniyya ne, a hirarsa da ‘yan jarida dangane da ‘yan hakika da ake cewa ‘yan darika ne, Shehin ya bayyana cewa, babu abun da ya hada ‘yan hakika da darika, domin ita dari babu wani haram da ta halasta, ya dai yi hanun riga da ‘yan hakika. KHALID IDRIS DOYA ya kasancewa a wajen ganawar ga kuma yadda hira ta kasance.

Akramallahu mene ne alakar Darika da ‘yan Hakika?

Ai ban sansu ba! amma an ce akwai wadansu mutane wadanda suke wasa da sallah suna wasa da matan mutane an ce koda Tijjaniyya suka soma ne, daga baya suka zarce suka kai wannan hakika din na raina musulunci, ba ruwanmu dasu, ba ruwansu damu. Su irin wadannan mutane, mutane wadanda shedan ya riga ya janyesu daga cikin yan Tijjaniyya daga cikin musulunci gabaki daya. wadannan mutane suna wasa da Sallah suna wasa da matan mutane wai ba komi, mu ‘yan Tijjaniyya dai muna gaya wa mutane a fili cewa Shehu Tijjani da ya kawo Darika abin da ya ce, idan ka ji labari an jingina wata magana ko wani abu daga gareni yake to ka aunashi da shari’a idan ya yi daidai ni na fada, in bai yi daidai ba ni ban fada ba’, Shehu Ibrahim Radiyallahu Anhu da ya gajesa ya ce to wannan fa Shehu Tijjani ya ce, mu yi ta karatu kenan, don in baka yi karatu ba yaya zaka yi ka gane gaskiya da rashin gaskiya cikin shari’a, Shehu Ibrahim yana cewa. “Na gode wa Allah cikin manyan alherorin da ya yi mini ya kiyaye mini zuciyata, ba za a ganni na karkata wurin abin da bai halatta cikin musulunci ba. Shin zina halal ne cikin Musulunci? Haramun ne babbar kaba’ira, wasa da sallah halal ne cikin Musulunci? Shi ma haramunne cikin Musulunci, saboda haka duk wanda ya ce shi almajirin Shehu ne to zamu duba mu gani yana bin hanyar Shehun, in suna sabawa shari’ar musulunci su ba almajiran Shehu bane don Shehu ba ya halatta haramun, don ita darikar Tijjaniyya ba wani abu sabo da ta kawo cikin shari’ar Musulunci, kuma ayyukan da Tijjaniyya ta kawo guda hudu ne daya sunan sa lazimi da ake yi safe da yamma, daya sunansa wazifa, daya kuma shi ne zikirin jumma’a sai kuma sharuddan da sai an fada maka ka yarda kafin a baka darikar, amma duk maganan daya shafi halal da haram Tijjaniyya nan ta samesu nan take binsu duk wanda ya canja haramun ya ce halal ne ya yi ridda ya karyata alkur’ani, ya karyata Manzon Allah (S) ba maganan darika ake masa ba wannan maganan ridda ake masa Allah ya ce, “Ko kusa da zina kar ku yi” kai kuma ka ce ba komi wannan riddance, haka kuma masu kamanta Shehu Ibrahim da Allah shi ma Ridda kun taba ganin Allah da Uwa da Uba? Shehu Ibrahim sunan mahaifinsa Abdullahi sunan mahaifiyarsa Aishatu, kuma ya rasu duk mutumin da yake da uwa da uba shi ba Allah bane.
 Kuma Allah yana mutuwa ne ? Allah rayayyene baya mutuwa, Ire-iren wadannan mutane a yi nesa dasu sun ridda su wadannan irin mutane ba ruwanmu da su, idan nace basa cikin musulunci ma na fadi gaskiya don sun karyata ayoyin alkur’ani da hadisan Manzon Allah (S).
Don ita Darika fa bayan mutum ya bi Malamansa sun koya masa alkur’ani, ya bi Malamai sun koya masa Ilimi sai kuma ya nemi Malamai masu gyaran zuciya, shi ya sa muka bi Shehu Ibrahim din kuma ya fi kowa kokari wajen bin shari’a da halalta halal da haramta haramun kamar yadda Allah da Annabi suka yi umurni.

Sojoji sun nusar da cewar ‘yan hakika sun bayyana a wasu sassa kuma ana dai cewa su ‘yan darika ne?

Sai su nemesu ta can domin suba ‘yan Tijjaniyya ba ne kamar yadda na fada muku tun farko, Dukkan wanda ya ke wasa da sallah ya ke wasa da azumi ya ke wasa da farillai ai baya kusa ma da Tijjaniyya domin ya yi ridda, mu kuwa ‘yan Tijjaniyya kowa ya sanmu mun fi kowa kokari wajen kulawa da sallah da yinta a cikin jama’a. Ba ma wasa da dukkan rukunan Musulunci, kuma muna nisantan dukkan abin da Allah ya haramta, wadanda suke wasa da sallah da matan mutane sun ridda domin sun karyata alkur’ani, sai su neme su can amma su ba ‘yan Tijjaniyya bane.

Shehi idan muka juya kan yawaitar kashe-kashen da ake samu a wasu sassan kasar nan me za ka ce ne kam?

Wannan tambaya na da muhimmancin gaske don amfanin gwamnati kiyaye rayukan ‘yan kasa, da gabobinsu da dukiyansu da mutuncinsu, da iyalansu in aka samu gwamnati ba ta kare rayukan mutane, ba ta kare mutuncinsu, ba ta kare iyalansu ba ta kare gabobinsu to hakika da saura, saboda haka muke kira ga duk wadanda abin ya shafa wato Allah ya dora muku amanar al’umma wato amanar ‘yan kasa, da rayukansu da dukiyansu da dukiyar da gabbansu wato jininsu da iyalansu da mutuncinsu wajibi ne a kare musu shi ne ma’anar gwamnati din. Su kuma ‘yan kasa su taimaka, cikin jin maganar gwamnati da biyayya wa gwamnati, idan an samu haka za a samu zama lafiya.

Annabi (S) wanda duk maganarsa a Ilimince ya ce, wajen neman zama lafiya dole ne manya su ji tausayin kanana dole ne kanana su girmama manya, kuma a girmama Malamai wadanda suka zama magada Annabawa, kuma ya ce duk babban da bai ji tausayin kanana ba duk kananan da basu girmama manya ba to ba sa tare da Annabi Sallalahu alaihi Wa sallama, ba wai an koresu daga Musulunci bane, a’a an koresu ne daga majalisar Annabi, inda mutane suke zama tare da Manzon Allah, saboda haka muna kiran manya su ji tausayin kanana, kanana kuma su girmama manya, su kuma Malamai a basu hakkinsu na magada Annabawa. In an yi haka za samu zama lafiya mai daurewa.

Amma kara zube kamar yadda ake yanzun nan wannan ya kashe wannan wancan ya kashe wancan kamar ba gwamnati, wannan ba shi da kyau.
Amma wassu na jingina wannan kashe-kashen ga addinin ko siyasa akwai kanshin gaskiya a wannan mahangar?

A’a kashe-kashen mutane a danganashi da addinin kuskure ne, shi addinin ya fi kowace jama’a kiyaye rayukan jama’a, da dukiyoyin jama’a da iyalan jama’a da gabobin su jama’an, to yaya kuma addinin ne zai bada umurni ana karkashe mutane ana tarwatsa musu dukiyarsu da iyalansu da mutuncinsu da jininsu? Ai addinin ba zai ce haka ba kuma bai taba yarda da haka ba, kuma kowani addini, addinin musulunci shi ne a gaba, sai addinin kirista shi ne mai biyo wa to duk wadannan addinai basu yarda da a kashe rayukan musulmi a kashe rayukan mutane, a zubar da jinin mutane, a wawashe dukiyar mutane ko’a kona ko a tarwatsa iyalansu, ko a hana musu ‘yancinsu na zama lafiya wannan ba daidai bane.

Kashe-Kashe nan ma ana akanta na Jos, Zamfara da Binuwai ga Fulani ina gaskiyar hakan?

Fulani ai ba baki bane a kasar nan shekara da shekaru Fulani suna nan a kasar nan da suna yin wannan kisan ai da ba yanzu ne za su yi ba da tun tuni suna yi, akwai dai wadanda suke yin haka suna fakewa da sunan wata kabila don su bata sunan wannan kabilar, an ce wadannan kasha-kashen da ake yi an ce da bindigogi ake yi, Fulani waya basu bindiga abin da suke da shi shine sanda da kwari da baka, amma basu da bindiga su Fulani,
Ko akwai shawara da Shehi zai bai wa a’lumma a kan wadannan mutane ‘yan Hakika?
Shawarar ita ce, koda an ji wani mutum ya danganta ‘yan Hakika da ‘yan Tijjaniyya a ce masa ba haka bane, mu ‘yan Tijjaniyya ba ruwanmu da ‘yan Hakika, don ‘yan hakika suna halatta haramun suna wasa da matan mutane suna wasa da Sallah, mu kuwa ‘yan Tijjaniyya mun fi kowa kulawa da Sallah mun fi kowa kulawa da abin da Allah ya halatta, mu mun barranta da su ba ruwanmu dasu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: