Sunday, 29 July 2018
Shahararen Jarumi Sarki Ali Nuhu Ya Bayar Da Kyautar Lambar Yabo Ga Dr Abdullahi Ganduje ( kalli Hotuna)

Home Shahararen Jarumi Sarki Ali Nuhu Ya Bayar Da Kyautar Lambar Yabo Ga Dr Abdullahi Ganduje ( kalli Hotuna)
Ku Tura A Social Media
Fitaccen jarumin wasannin shirin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya gabatar da kyautar lambar yabo ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahu Umar Ganduje.

 Ali Nuhu ya mika kyautar ne ga gwamna Ganduje da yammacin yau, Asabar, a fadar gwamnatin jihar Kano yayin gabatar da wani shirin wasan Hausa, MUTUM DA ADDININ SA, da aka shirya domin karfafa gwuiwa da ilimantar da jama’a a kan hakuri da juriyar zama da wadanda ba addininsu daya ba. Sarki Ali Nuhu ya bawa gwamna Ganduje kyautar lambar yabo

Share this


Author: verified_user

0 Comments: