Wednesday, 25 July 2018
Sakon Buhari Ga 'Yan Majalisar Apc Da Suka Koma PDP

Home Sakon Buhari Ga 'Yan Majalisar Apc Da Suka Koma PDP
Ku Tura A Social Media

▪Babu Wata Rashin Jituwa Tsakanina Da Daya Daga Cikin Masu Canja Sheka

Ina fatan alheri ga 'yan majalisar APC wadanda suka canja sheka zuwa PDP a yau kuma jam'iyyar APC ta yi iyakacin kokarinta wajen ganin ba su fice daga jam'iyyar ba, don haka Ina jinjinawa shugabanni APC bisa kokarin da suka yi na hada kan 'ya'yan jam'iyyar.

Ina da tabbacin cewa wannan mataki da 'yan majalisar suka dauka ba zai cutar da farin jinin jam'iyyar ba saboda haka ina kira ga sauran 'ya'yan jam'iyyar kan kada su tayar da hankularsu, don dama a kan samu irin wannan yanayin da zarar lokacin zabe ya karato.

Na san cewa mafi yawan 'yan majalisar masu canja shekar, suna da matsaloli a mazabunsu musamman ma tsarin karba karba zai hana sake tsayawa takara.  Ina jaddada cewa babu wata rashin jituwa  kai tsaye tsakanina da daya daga cikin masu canja shekar kuma ni ban riki daya daga cikinsu a cikin zuciyata ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: