Monday, 16 July 2018
Kalli Hotuna: An hango sanata Kwankwaso a coci ranar juma'ar data gabata ba bu jar hula

Home › › Kalli Hotuna: An hango sanata Kwankwaso a coci ranar juma'ar data gabata ba bu jar hula

Post By:

Ku Tura A Social Media

Daga Musa Abdullahi Minista

A ranar juma'ar da ta gabata ne wasu hotunan tsohon gwamnan Kano kuma sanata mai ci, Rabi'u Musa Kwankwaso, suka fantsama a dandalin sada zumunta daban-daban inda aka hange shi a cikin wata Coci ba tare da jar hularsa sanye a kansa ba.

Abu biyu da suka bawa jama'ar dake yawo da hotunan na Kwankwaso a dandalin sada zumunta mamaki sune;

Ganin shi babu jar hula da kowa ya san shi da ita da
Da kuma kasancewarsa a Coci a ranar juma'a da Musulmi ke zuwa masallaci.

Ganin Kwankwaso a Coci ba wani abun mamaki bane idan aka yi la'akari da kasancewarsa shugaba kuma mai burin zama shugaban kasar Najeriya dake da yawan mabiya addinin Kirista.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: