Sunday, 8 July 2018
Kadarorin da shugaba Buhari ke harin kwacewa, sunayen gwamnnoni da Ministoci, na da da na yanzu

Home Kadarorin da shugaba Buhari ke harin kwacewa, sunayen gwamnnoni da Ministoci, na da da na yanzu
Ku Tura A Social Media


Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yasa hannun ne domin cigaba da yaki da rashawa - Da tabbatar da dokar, Buhari na harin kadarorin da aka mallaka ne ta hanyar satar kudin kasa kuma aka aje su a gida Najeriya ko a kasashen ketare

 - A jerin sunayen da majiyar mu ta gani, sama da tsofafin gwamnoni 10 ne ke fuskantar kuliya akan zargin su da ake na mallakar kadarorin ta hanyar sata 
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis yasa hannu akan dokar zababbu mai lambar umarni na 6 dake harin kadarorin tsofafin gwamnoni 11,Ministoci da kuma wasu sanannun yan siyasa wadanda sukayi mulki tsakanin 1999 da 2015.

 Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yasa hannun ne domin cigaba da yaki da rashawa. 
Da tabbatar da dokar, Buhari na harin kadarorin da aka mallaka ne ta hanyar satar kudin kasa kuma aka aje su a gida Najeriya ko a kasashen ketare. 

A jerin sunayen da majiyar mu ta gani, sama da tsofafin gwamnoni 10 ne ke fuskantar kuliya akan zargin su da ake na mallakar kadarorin ta hanyar sata. Jerin kuma ya kunshi mutane 155 da ya hada da yan siyasa, yan kasuwa, manyan jami'an gwamnati da kamfanoni da akayi amfani dasu duk suna cikin jerin.

  Tsofafin gwamnonin da ake harin kadarorin su sun hada da: Gabriel Suswan, Danjuma Goje, Alao Akala, Dr. Babangida Aliyu, Sule Lamido da Gbenga Daniel. Sauran da ake harin sun hada da : Attahiru Bafarawa, Orji Uzor Kalu, Saminu Turaki, Chimaroke Nnamani, Fintri Amadu. Dokar tana da burin karbe kadarorin tsofafin ministoci karkashin mulkin Goodluck Jonathan da Obasanjo, da suke fuskantar shari'a. 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: